Pages

Friday 29 June 2018

Page 7of KAZAMA CE MATATA

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*KAZAMA CE,MATA TA*
           ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
Written by Ganarious✌๐Ÿป
     7

√...One love keep us 2geda, masu bin wannan labarin.

√... @ mss-ganarious (instagram)

√...ganarious98@gmail.com
√...ganarious book series (facebook group)
√...ganarious.blogspot.com/
        Duk zaku iya droping comments dinku, a daya daga cikins๐Ÿ‘†๐Ÿผ,thanks

     **       **       **       **
Bayan kwana uku da kawo wa suwaiba kayan shayi,kwance take a doguwar , sai sharban bacci take abinta, kai da ka gan ta kasan bata da damuwa, lau lau take.

Daga bakin kofa yake kwada sallama,ganin ba'a amsa ya sanya shi kunno kai,sabida kofar a bude take.

Duban falon yakeyi sama da kasa,sai da ya gama kallon falon tsaf, sa'anan ya nemi guri ya zauna, tare da tsira mata ido.
Ya jima zaune,cike da takaicin yanda ya tarar da gidansa.
A hankali ta bude idanunta, dai kan nasa...ta saki murmushi tare da mikewa zaune...."laaahhhhh, zuwa ka kenan muniru?

Fuska tamke ya ke kallonta ba tare da ya amsa ba.
"sannu da isowa ta dake fadi"
Nan ma bai amsa ba.
Ganin haka yasa ta mike...."bara  na kawo maka ruwan sanyi ko?
No... No....koma ki xauna muyi wata magana.

Xama tayi tana dubansa.
"ko kina iya tina maganar da na fada maki, a lokacin da kika zo nan gidan?

Eh kwarai......
Toh fadi naji, me na fada maki.

Cewa na kayyi na dunga sallah akan lokaci.
Da me kuma?
 Kacce kuma baka kaunar kazanta.

Toh meye sa kike kazanta?
Ni yaaaa......ta fadi hakan dafe da kirjin ta.

Kallon ta kawai, yake ba tare da ya ce wani abu ba.
"kazantar mi nayi halan, daga dawowarka sai ka lakarmin cewan ina kazanta?  ...dubi falon nan fa fes fes na share ta.
Duk ko wane sako na share sa'anan ka dube ni kace ina kazanta? Amman dai kam baka da godiya.

Keh....ya fada a tsawace a yayinda yake dakatar da ita,...."idan bikiyi hankali ba, zan maida ki gidanku...shashasahhah,duba fa ki gan yanda kika maida min gida,? Inai maki  magana kuma kiyi min fitsara?
Mikewa yayi a fusace ya nufi sashensa.

Bata sake sanya shi a ido ba, sai washegari da safe ya dawo daga massallaci sallar asubahi.
Tana ganinsa ta gaida shi.

Shi kuwa gogan da kyar yake   amsa mata gaisuwat.
Kai tsaye dakinsa ya wuce.....kamar kullum, yayi azhar da karatun al'qur'ani me girma sa'anan ya sanya kananan kaya ya fito zuwa kitchen.

A nan ya tarar da abin mamaki....a hanzarce ya nufi sashen ta cikin bacin rai.
Kwance ta ke, da ka gan ta kasan bata da damuwar komai.
Da tsawa yayibkiran sunanta
A firgice ta mike tana me murzan idonta.

...."me ke damun kwakwalwarki? Ke wacce irin mace ce?....watau ke baki jin magana ko?  a jere yake wadanan maganar,ba fusstop ba comma.

"mi na na kuma nayyi?
Ya sa hannunsa, ya riko hannunta ya me janta da karfinsa,saura kiris, ta fadi
Kitchen ya nufa da ita... "what's this? , what's all this, for God sake.

Ni fa ban gane mi kaka nufi ba,ka fada min laifin da nayyi...wanan tsawon yana bani tsoro.

Lumshe idanu yayi, tare da yin ajiyar zuciya.
A hankali ya bude su, sukai ido hudu, domin kuwa itama shi din take kallo.

Dubi nan.....ya nuna kasan kitchen,inda ta hasa murhu.
Duban gurin tayi, sa'anan ta da'ga ta dube shi suka sake hada ido.
Sun da'de suna duban juna, sa'anan ta nisa yace inda nake girki kenan.

Wannan kitchen din yayi maki kama da inda ake girkin itace?

'"yo shin ina na zaniyi girki,shin ba kai na kaccemin  dakin girki ba ne kenan?...ita din cikin bacin rai take maida masa,don ganin itace mai gaskiya

Ya kai kimamin minti uku, ya na dubanta sa'anan ya saki hannunta.
Murya kasa kasa yace "suwaiba"

Na'am...
Kina kallon fim ko ta hausa, ko kuma ta yan yare kamar ta indiyawa?

Sosai ma kuwa ina kallon su.
Kina ganin dakin yin girki a fim din da ki ke kallo?
Kwarai ina gani.

Kin taba ganin kitchen makamacin wannan?
Eh...amman a fim din turawa nake ganin irinta.

Yawwa......toh a fim din da kike ganin wannan irin kitchen suna girki fa itace?

Shiru tayi, tana dubansa...
Ke nake sauraro!

Toh ni wallahi, nayi nayi abin can ya kunnu, ya kiya.kuma yanda ka nuna min hakan nayi, ganin bai yi ba, shi yasa na hasa murhu.

Ajiyan zuciya yayi....ya tina shi din ne bai nuna mata yanda ake kunna switch din gas din daga cylinda ba.

Toh naji wannan.....mi ye sa baki tsaftace gurin ba, bayan da kika gama girkin? Duba fa  ki gani gurin nan bashi ba banbanci da bola,ya na maganar ne a yayinda yake nunin gurin da yatsa..ledan maggi,bawon albasar da ya'yan tattasai, har da kamu-kamun tawaska da ta diddiga a gurin Da sauransu.

Niyah ta yau na kwashe su.
Cikin girgiza kai yace..."kar ki sake.!! Daga yau kafin ki fita a kitchen, duk wani abu da kika yi amfani da, da gurin da kika yi girkin,toh ki tabbata kin tsabtace su....kina ji na?
Awo..... Ta fada.

Hannu yasa ya rike kunnensa,..."duk ranar da na sake ganin kitchen din nan a haka, a ranar bazaki kwanan a wannan gidan ba.kinji ko?

Mi na na yayyi zafi haka, bazan ma sake ba, balle kace na tafi gidan mu.

Nan ya shiga kwasan itacen, da dutsinan.
Sai da ya tabbatar da kitchen din yayi fes, sannan ya fita.takaicin sa daya, tiles din  indabta hasa murhun ya kone,sai yayi daban da sauran.

Kashe gari bayan ya gama Azkhar  dinsa,yayi wankan sa, sai da ya shirya tsaf,sannan ya fito rike da brief case dinsa.
Zama yayi gurin dininng. Shiru shiru, bai ji motsin ta ba,don haka ya mike zuwa kitchen.
Daga alama, ba a shiga kitchen din ba ma.
Ya karasa  ciki,ya zuba tuwa a kittle ya kunna.
Tsaye yayi yana me jiran ruwan yayi xafi.
Kofi ya dauko, ya dan dauraye tare da zuba ruwan zafinsa,ba yan da ya yi zafi.
Ya dauko kofin zuwa gun dininng table, inda kayan tea suke.
Ya dauko madara da bonvita ya bude marfinsu, nan mamaki ya rufe shi.
Ya karkada kai, tare da fadin Allah yayi mana sauki.
Ya xuba madara da bonvita a kofin ruwan zafin ya karkada,ba tare da ya hada da burodi ba ya kafa kofin a baki, sai da ya shanye, sanan ya sauke kofin.

"Ahhhh....Alhamdulillah, ya fada a yayinda ya mike zuwa kitchen din,ya wanke kofin ya maidashi inda ya dauko sannan ya fito zuwa office.

Da isan sa office abokan aikinsa suka soma zolayansa.
Wasu na fadin ango ka sha kamshi...wasu na fadin ka sha mai da dai sauran su..
Zuciyarsa ta kusan tsagewa, a lokacin da wasu ke fadin "yaushe za mu zo ganin amarya,mu kuma ci girkin amarya?
 Dariyar ya'ke kawai yakai, a zuciyar sa kuwa fadin yake "tabbas ajina zai zube, idan suka zo suka gan irin matar da na ke aure.

Gidansa ya nufa, bayan da ya tashi daga gun aikinsa.
Kwance ya tarar da ita, wannan karon idon ta biu, ma'ana ba bacci takeyi ba.
Tana ganinsa ta mike zaune...."barka da dawowa ta  fada.
Yawwa, ya maida mata a yayinda ya nufi sashen sa.
Mikewa tayi zuwa kitchen, jim kadan ta fito rike da kulan abinci ta ajiya saman tebur.
Ta koma cikin falon ta zauna.ta kai kimamin minti goma zaune, bai fito ba, don haka ta nufi hanyar sashen sa.
Karo na farko kenan da zata shiga dakinsa.
Da sallamarta ta bude kofar,ba tare da ta jira amsa ba, ta kunsa kai.
Ganin bashi cikin dakin yasa ta karasa gun gadon sa,ta shiga ta'bawa tana shafansa,daga nan kuma ta daga kai tana me duban ilahirin dakin.
Waigowar da zatayi gefen hagunta, yayi dai dai da fitowarsa daga bayi.
  Daure yake da tawul,iya gwiwansa.suna hada ido, ta kau da kai tare da sanya hannunta ta rufe ido...don Allah kayi hakuri, walle bansan cewan kana bayi ba, daman na zo ne na  fada maka cewan abincinka na bisa tebur na ajiye.

Tsaye yayi yana kallonta ba tareda ya ce wani abu ba.
Ya ratsa ta gefen ta zuwa gun wardrob nasa, yar karamar tawul ya ciro.ya shiga goge kansa da jikin sa.

SUWAIBA hooo.....wai fa idan ta a rufe ta ke tafiya zata bar dakin.
Bata ankara ba tayi karo da wata kyakyawan tebur, me tsawo.gefen teburin wata yar doguwar gunki ce ta ado..wannan gunki duk da gilashi aka kerata, don ya zama wa engr. Munir madubin dubawa..
Bayan da tayi karo da teburin, ita kuma teburin ta shike akwai taya a kasarta don haka tayi tafiya zuwa  gunkin,ta buge ta..
Nan gunkin tayi batun fadoea suwaiba, tsaye tayi bayan da taji cewan ta kauri abu...ba ta kuma bude idonta.

Ganin abinda ke shirin afkuwa ya sanya shi barin gun wardrob dinsa a guje har tawul din jikinsa ya sulbe.
Kafin duk gunki ta fadowa suwaiba,ya rikota da karfinsa ya janyo ta jikinsa suka fadi.
Tas...tararassss kawai kake ji,gunki ta tarwatse.
Sai a lokacin suwaiba ta bude idon ta,ta gan kanta a jikinsa.
Kokari take ta zame jikinta daga nasa, tana mikewa ta gan ba bu ma tawul din a jikinsa, ...."subhanalillahi ta fada da karfi a yayinda ta rintse ido tana sauri zata bar dakin.
Fisgo ta yayi..."keh...ya fada a tsawance,ke wace irin marar hankalice,ba ki ganin gilashin da suka tarwatse a kasa.
Idon rufe kika yi sanadi,yanzu kuma idon ki a rufe kike son fita daga dakin don ki yiwa kanki illa ko?

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.