Pages

Tuesday, 26 December 2017

Un-name story.

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.
    Godiya da yabo sun tabbata ga ubagijin talikai,mai rahma mai jin kai,mai amsa addu'ar wanda ya rokeshi.

        SANARWA..!!!
Wannan takaitacen labari kirkirarene...ba'a Samata suna ba sabida marubuciyar tanason ji ra'ayin ku.ma'ana duk wace ta karanta ta kuma fahimci wani abu daga wannan labarin sai ta sa mata sunar da duk tagan ta dace da ita(akan  fahimtarta)..da haka zatayi anfani da "majority' respond daga makaranta,don sanyawa littafin suna dakuma yin ful version din..zaku iya droping comments/contributions da kuma sunar da kuka gan ya dace da littafin a 👉🏼Ganarious.blogspot.com/
Godiya nake.😇

        DEDICATION..!
this short story  is been dedicated to the honest women in the world. GAISUWAR SADA
 ZUMUNCI.
*Zuwa makaranta,
*groups,
*marubuta,
*the good women &
*all others,Assalamu-alaikum.
      ®2017
Biye take dashi a hankali ba tare da ya lura ko fahimci haka ba.

Arkilla suka nufa,duk dai tana biye dashi..tayi mamaki ganin sun sha kwanar junction din gidansu kaka..sai kuma ta basar tare da yin hamdala,ko ba komai gidan sauki na zo domin kuwa zan su binciko min yarinyar da officer ke zuwa gunta.

Tunda suka kuno kai ta rage binsa,tana dan nesa dashi...
Dai-dai kofar gidan kaka yayi parking,itama guri ta samu tayi parking tana me kara mamakinsa na parking gidan kaka.
Tana cikin mamaki,sai ta hangi wata kamar JUWAYRIYAH tare da wata sun fito daga cikin gidan kaka.

Ta fito daga motan tayi dan taku kadan daga inda tayi parking zuwa gaba,tana son ta tabbatar ne ko JUWAYRIYANCE..

tabbas itace don kamar ance ta juyo,ita wacce suke tare ta wuce abinta,ita kuma JUWAYRIYAH ta shige motan officer.

Ta dade tsaye tana mamaki abinda ya kawo officer gun JUWAYRIYAH...Tayi kutta tare da fadin zaki gane kuranki,watau ma dake za'a hada kai a cutar dani ko!.daman kinsan wacce officer ke zuwa gurinta amma baki ta'ba sanar dani ba ko?
Ita kadai ke surutun ta..tana gamawa ta shiga motar ta ta tayar.
A guje ta shigo gidan tana me kwalawa kaka kira da karfinta...kaka..kaka...kaka!!
Tana shiga falon ta tarar da ita zaune tayi tagumi.
Hannu ta sa tacire tagumin tana yarfa mata bundir din dubu daddayan da ke hannunta.
Cikin farinciki tace kaka ga wata dubu darin kuma,tana fadin haka tana shafawa kakar kudin a kuncinta.

Ita kuwa kaka sai binta take da ido.
Guri ta samu ta zauna tana facing kakar tace"inayi maki magana kin kyaleni"

Ajiyar zuciya kaka tayi tace yar nan na fada maki kar ki yi haka,wallahi anty hafsatu bata cancanci haka daga garemu ba.
Kiyi hankuri ki bar zancen wannan mutumin,Allah zai kawo maki wanda ya fishi

Kai kaka!so nawa zani fada maki da ki daina damuwa da zance anty hafsat!.don kawai ta taimaka  mana sai ace kar muji dadin rayuwa..toh gaskiya sabida ita bazan yi denying abinda nake so ba..besides shi ya ganni yace yana so.
Sa'anan da ya je ya auri wata bazan daga waje tazo ta cutar da ita ai gwara ni na shiga ma'ana ya aureni..kinga ba yanda za'ayi na cutar da ita ok?..ta dagawa kakar gira..
"Duk da hakan dai hankalina bai kwanta ba"inji kakar.

Ta yamutsa fuska tace "bari na fadamaki kaka,idan zaki kwantar da hankalinki ki jidadin sauran kwanakin da suka rage maki,ki kwantar.duniyar ce daman kuma haka ta ga'da.
...ba abinda anty hafsat zatayi mana da ya wuci ta yi fushi ko ta yanke zumunci da mu,bayan nan kuma fa?..ta yarfa hannu tana me kallon fuskar kakar tace "Babu".

Ajiyar zuciya kakar ta sake yi ba tare da tace wani abu ba.

JUWAYRIYAH ta mike zuwa daki,ta fito rike da wayarta...Aminiyarta ta nemo,bugu daya zuwa biyu ta dauka.bayan sun gama gaisuwasu irin ta shakiyannan take tanbayar kawarta yaushe zata shigo ne.
daga dayan bangaren  take sanar da ita cewan"nifa a bushe nake,bana maganin sisi.
..."kar ki badani mana" kamar ba nice aminiyarki ba" ai idan na samu kamar kin samu kenan.

..kai kawalli!..na ji kamshi wani abu daga wannan furucin.

Cikin dariya tace sai dai kinzo,ki shigo gobe da safe muje kasuwa..daganan ta kashe wayan.
Ta juyo ta dubi kakarta da tunda ta soma waya take kallonta.
Cikin murmushi tace "kakus-kakus...da me dame kike bukata?,idan naje kasuwa na sayo maki.
Cikin girgiza kai tace ba komai..
Ba tace mata komai ba ,ta zari mayafinta ta ficewarta.

  Sai bayan sallan magrib ya shigo gida kamar kullum dai.
Yauma ta nufeshi ta amshi jakar hannunsa.
Ta taimaka masa yayi wanka ta fito masa da dogon riga marar nauyi,ta fesheshi da turaren KHUD.
tare suka jero zuwa dining,ta zuba masa abinci a plate tace bisimillah sa'anan suka fara ci.
SOsai ya ci abincin hakan ya nuna yana tare da empty stomach...
Bayan ya wanke hannunsa yayi hamdala sa'anan ya tashi daga gurin dining din zuwa cikin falon.
Ta kwashe kwanukan da suka ci abincin tare da kintsa gurin sannan ta biyoshi falon ta zauna kusa dashi.

Ya da'ga hannu ya rungumota jikinsa,nan tayi lamoo....
Cikin sarkewa murya yace "ayimin hira me dadi mana".

Har cikin ranta,taji dadi da ya fadi haka.don da'ma tunda suke cin abinci take son tambayarsa abinda ke kaishi unguwarsu kaka,sai dai kuma bata son yace tayimasa shisshigi,don haka wannan maganarsa ta kawo mata opportunity.
Tayi murmushi tace yau kam ba hira me dadi!
...ya dube ta yace sai marar dadi?
Tayi dariya har kyawawan hakoranta suka bayyana...
Ya sake fadin "yau miye sa ba'a sami hira me dadi ba?
...hmmmm,maza tsoro suke bani.

Da sauri ya juyo yana dubanta cikin mamaki.
Ta da'ga masa gira tare da fadin yau wani labari naji a gun aikinmu da ya taba min zuciya...

Kamar jira yake ta kai maganar,yace miye faru?

Ta ta'be baki tace wata ce da muke aiki tare..
..ba tareda ya bari ta karasa maganar ba ya tare ta da fadin miye sameta.?
...hmmm,kawai ta fada sannan tace banason maganar ta dame kamar yanda ta dame tare da sanyayamin jiki...yau duk a kasale nake sabida abinda ya faru da ita.

Cikin kosawa yace "pls can u just go straight to d point?..na matsu wallahi.

Gyara zama tayi,ta rasa me zata fada masa don daman dabaru takeyi don riga kafin abinda tage hangowa...can sai ta tuno da labarin wata mata,nan da nan ta fara.
   ...watace a gun aikin mu,sunan ta halima,muna kiran ta madam halima ko malama....yara uku,duk mata.
Mijinta ya samu wani incident tun shekaru goma sha bakwai da suka wuce.A lokacin yana aiki da wani attajirin me kudi. Aikinsa shine bin wannan mutum duk inda za shi ko kuma aike watau massenger.
Watarana attajirin ya aikeshi,yana cikin tafiya wasu suka tsayar dashi a kanhanya.sun duba plate number motan suka ce shine...da jin haka sai ya rude yana fadin wallahi ba ni bane ba motana bane ni dan aikene..basu saurareshi ba suka turashi cikin motan tare da dauke jakkan kudi,ganin haka yasa shi karfin halin kokawa dasu wai shi zai amshi jakkar,nan suka yi masa duka,sai da suka gan alaman baya numfashi sa'annan suka saka shi a motan tare da sawa motan wuta.

Idan kwanarka bai kare ba, ba yanda za'ayi ka mutu,wannan bawan Allahn Nan bai mutu ba amma kuma ba shi da banbanci da gawa...sakamakon dukansa da sukayi ya sami matsalar kashin baya,megidansa ne ya taumaka aka tafi dashi kasar india domin gyaran  kashin.
baya n nan kuma bai sake bin ta kansa ba,balle ya dauki nauyin sauran treatment din ko ta iyalansa.
Madam Halima ce ke komai,daga kan kulawa da yara,aminci gida har kudin asibiti..domin kuwa bayan sun dawo daga kasar india asibiti aka sauke shi don gyaran fatarsa.
Madam Halima ta shekara uku tana tare da gawa' sabida ko motsi ba  yayi balantana bude ido sai numfashi kawai hakan kuma baisa  ta fasa auren ba...duk wani abu nasa ta sayar,har ita din ma bata komai sai kaya kala uku sai kwanuka daidai su,tayi kosan sayarwa,tayi talla,tayi wankau duk dai sabida ta sami abin kaiwa asibiti...shikuwa mijin bai san duniyar da yake ba.
Duk da mawuyacin halin da tashiga yaranta na zuwa makaranta.

Tana cikin wannan yanayi likitoci suka bukaci da ta kawo kudin da ake binsu,sa'annan ta kawo kudin aiki,idan ba haka ba tohh su tattara su koma gida...ta sake shiga wani hali,nan ta shiga gari tana neman taimako da aro a gun jama'an gari,har yan uwan mijinnata amma abu guda take ji"Babu"..tayi kuka ta baiwa Allah komai.
A daren da za'a sallame su,ta fito ko Allah zai hada ta da wanda zai taimake ta,tana cikin tafiya ta hadu da wani makwabcinsu,shi wannan makwabcin nasu dan kwaranda ne masu ginar kasa su ciri ko zinari ko azurfa da sauransu.
Bayan gaisuwan ta gabatar da bukatanta  nason ya ara mata kudi.
Ya ni'sa ..yace a gaskiya bashi da kudi yanzun,amma akwai wani aiki da zasu tafi yi a jihar neja,idan dai tagan zata iya,sai ta bishi amma fa aikin akwai wuya...shi kadaine taimakon da zai iya yimata a yanzun.
Tayi ajiyan zuciya tace zan iya da yardan Allah.
Suna magana ta nufi asibitin,nan ta shiga basu hankuri yi masu alkawarin nan da wata biyu zata kawo masu kudin su.ta kuma nemi alfarman da su bar mijin ta annan,su kuma bashi treatment din da ya kamata.
Daga asibitin ta nufi gidan kanwar mijinta,ta nemi alfarman da ta ajiye yaran gunta tana duba mata su kafin ta dawo..kanwar mijin ta ba'ta rai ba tare da ta amsa ba.
Kashe gari da safe madam halima ta shiga bin gidaje inda suke bukatan wanki tayi masu ta amshi kudi ta je wani gidan,idan wanke wanke ko share sharene tayi su bata kudi..da hakan ta dan tara silalla,ta sayi wa  yaranta sabulan wanka na wanki,makilin da dai abunda zasu bukata..ta kuma sayi abinci ta kaiwa kanwar mijinta gudun kar nauyi yayimata yawa...ragowan kudin kuma tayi sadaka dasu tare dayin addu'an Allah shi maida mata baninki wannan.

A gurin ginar kasan ba irin challenges da bata gani ba,su biyu ne kawai mata,ita musulma dayat kristan...sai kuma maya masu kawo masu abincin saidawa.

Iya wulakanci da cin zarafi madam Halima ta gani...ta dai wulakantu.
Wani cikin manyan ogoninsu ya nimeta da harkan banza,ta sanar dashi ita matan aurece kuma me tsoron Allah,don haka taki bashin hadin kai,sanadin haka ya sanya mata ido,tare da kuntata mata..tayi kuka tayi kuwa ta kai kara gun me sama.
 A ko dayaushe tunaninta   na gun yaranta da babansu..bata san wani hali suke ciki ba.

Akwai wani guri dasuka auna,sun tabbatar za'a sami zinari a gurin,don haka aka shiga ginansa..kwana takwas ana gina gurin,ba alaman wani abu..kwana ta tara,wannan ogan ya hasala ya ce abar gina gurin a canza guri,don daga alama ba za a sami komai ba...don haka kowa ya watse don daman gari ya fara duhu.

Madam halima ta tashi zatayi qiyamulail,sai ta nufi inda sukayi ginar kasar don yin tsarki.
Tayi tsarkin ta,ta taso tana dawowa sai ta gan kamar abu na walkiya,ta yi addu'a a zuciyarta sa'anan ta karasa gurin.sai me zatagani!!!!!!!😳😳🤭
Diamond ne ta gani..tayi sauri ta sa hannu ta dauka,nan take tayi sujjada tana meyiwa Allah godiya..
Bayan ta bar gurin tashiga tunani yanda zata boyeshi ba tare da kowa ya sani ba.
Nan dabara ya fado mata,ta koma makwancinsu ta dauko allura da zaren da tazo dashi,ta yagi zanin jikinta ta dunkule dutsen ciki sa'anan ta dinke shi gam gam a jikin pant dinta.
Tundaga wannan lokacin take cikin farin ciki da anashuwa koda kuwa sun bata mata rai bata damuwa,fatan ta dai su koma lafiya.

A ranar da ta dira birnin shehu,a daren ranar  ta nufi babban asibitin da ke garin sakwato inda aka kwantar da megidanta.
Dakta mustafa yana daya daga likitocin dake kula da mijinta..yana tausayamata sosai tare da bata baki da kuma taimako iya karfinsa..don haka tana isa asibiti shi ta fara nema,nan suka sanar da ita yana off don haka ta nufi dakin da mijin ta ke kwance.
SHi kadai ta tarar ba kowa tare da shi,yanda ta barshi haka ta same shi..ciki farin ciki tare da hawaye  ta rike masa yatsa tana gaida kamar me jinta..tayi masa alkawarin komai zaiyi karshe da yardan Allahu..
Ba taje gurin da ta bada yaranta ajiya ba,ta koma gida.

Kashe gari da safe  ta nufi asibitin,a harabar asibitin sukayi karo da Dr.mustafa,sun gaisa ta nemi su ke'be,..bai musan ba,suka ke'be zuwa inda ba'a ganinsu.
Nan ta sanar dashi batun dutsen da kuma yanda akayi ta sameshi.

Ya tausaya mata tare da yi mata murna...ya nemi sanin ra'ayinta yanda zatayi da shi dutsen.
tace masa tana son ya taimaka mata a sayar da shi..nan yayi mata alkawarin zai yi abinda ya dace.

.....kudi masu yawan gaske ta samu bayan ansaida dutsen.
Dr.mustafan ta baiwa komai,don haka ya kawo shawaran tar da mijinta waje.
kasar jamany suka kaishi aka gyara masa fata da sauran kasusuwan yatsun sa da suka markwashe..tabi mijin nata domin junyarsa,suna can har ya bude ido....sai dai kuma kashh🤔🤨!..Megidan nata yayi loosing memory dinsa amman likitocin sun tabbatar mata na dan lokacine ba me daurewa bace.
kafin su dawo ta aikawa Dr.mustafa sako da ya saya mata gida madaidaici daman gidan haya suke zaune.
Bayan sun dawo ta sayi kaya ta sawa gidan.

Sannu a hankali mijinta yafara samu sauki.
Dr.Mustafa ya zo dubiya sai yake tambayar madam halima mi zatayi da sauran kudinta.

Shiru tayi daga baya tace  zata juya shi ta hanyar sana'a,sannan zan shiga makaranta na kuma biyawa yarana kudin makaranta.
Ya jidadi da ta fadi haka,don shi yana sah'awar mesonyi karatu..don haka ya bata goyon baya.

Bayan ta gama biyan bashisuka da ake binta ta biyawa yaranta kudin makaranta har zuwa lokacin da zasu gama..
Ta baiwa dakta,ya ki karba.
Ta sayi shago da sunar mijin,ta mallakamashi sabida ta sawa ranta idan har yaji sauki bazai karayin aiki karkashin wani ba.
  ...bayan an salleme su,sun dawo gida sauki kam sai hamdala domin kuwa memory dinsa sun fara dawowa..ita kuma alokacin ta sami karbuwa a makarantar shehu shagari college of education da ke garin sokoto..a yayinda take zuwa makaranta,yaranta ma suna zuwa..don haka makaranatar ta rabi da rabine,idan dai tana lecture hankalinta na gun mijinta,da zarar anfito sai ta dawo ta dubashi kafin lokacin wani lecture yazo ka kuma kara komawa,ganin haka  yasa Dr.Mustafa bata shawaran da ta sami wani wanda yayi makaranta irin su nursing school ko health school ya dinga zama dashi sabida bada magunguna da sauransu.
Ta kuwa yi sa'a,ta sami yar budurwa wacce ta gama health school ba aiki,don haka sukayi yarjejeniya da kuma abinda za'a dinga biyanta.

Cikin ikon Allah ya sami sauki sosai,har ya fara takawa daga nan ya fara zuwa shagonsa da ta bude masa.
Madam Halima ta gama makaranta,tayi dabaran yin degree dinta..bayan ta gama ta sami aikin koyarwa..cikin ikon Allah ta aurar da babbar diyarta.
Allah ya albarkaci shagon,har sun kai ga bude wasu manya.manyan shoguna suna sai da kayan electronic...arziki ya zaunu sai hamdala

Suna haka kwatsam madam halima taji mijinta ya kara aure...
😳😔😞😏😥😟😰

***tunda malama Hafsat ta fara magana,idon malam Zubair wanda take kira da officer na kanta.
.. ta dubeshi tace kasan ko wacece ya aura?
Ya girgiza kai alaman a'a.
"Wannan Nurse din me kula dashi".
Yayi ajiyar xuciya ba tare da yace wani abu ba.
Ta kara tanbayarsa da fadin "don Allah ya kyauta mata kenan?"
Shiru yayi daga baya yayi gyaran murya yace "yace yanzun haka ba gaskiyan labarin ba kenan!.ko kuma itace bata da gaskiya har ya kai ga yin hakan.

😳😳huh..! Kamar ya fa?.ta sake tanbayarsa.
Uhmmm...kinsan mata!.
Yanzun haka bata fadi the other side ba ma'ana,duk cikin labarin bata fadin inda tayi mistake ba,so ba ku taba fadin laifin ku sai dai na megida sabida mutane suyi blaming dinsu...itah fa wannan madam halima tunda itace sanadiyar arzikinsu ta iya tayi masa gori ko kuma taso ya zama karkashinta..she might want to be the BOSS👸🏻
shi kuma kila bazaiyi tolerating ba sai yayi hakan.
C'mon officer..what so ever it is ya kamata ace yayi aure bata sani ba?.?
Shiru yayi..ta ta'be baki tace "ashe zaka iya yimin  hakan kenan,..sabida labarina da strugles dina da nata suna da kamanin"..shiyasa jikina yayi sanyi yau throughout.
murmushi yayi ya janyota jikinsa..Haba my soul ya'ya za'ayi nayi maki hakan,ai sai Allah ya kamani..
Ta juyar da kai gefe tace 'atohh don nasan maza basu da tabbas."

A daren ranar tanajin motsi motsinsa ,da alama maganar/labarin ce ta shige shi,don har bacci yayi awon gaba da ita bai runtsa ba.

Kashe gari da safe suna breakfast ya da'go yana dubanta tareda fadin"idan da kece haka madam Halima ya ya zakiyi?
Chak!🙄..ta tsaya tana dubansa,sai kuma ta hadiye abincin dake bakin ta tace "me zanyi??
 Ya da'ga  mata kai.
Tace uhmmm..kawai tace,tacigaba da cin abincinta ba tare da ta amsa shi ba.
Suna kammala cin abincin,ta kwashi kwanukan.
     **     *        *    *       **
A gidan kaka kuwa  da safe,JUWAYRIYAH ta hada masu kayan breakfast nagani a fada,masu lafiya da gina jiki.
karfe goma sha Daya dai dai kawarta kuma aminiyarta basma  tayi sallama ta shigo sun rungume juna  cikin murna suka shiga falo.
Basma ta bude baki tana fadin ashe an gyara maku gida??
Ta riko hannunta ta zaunar da ita tana fadin kodai na gyara gidan.
Cikin mamaki Basma tace  ke kiga gyara kamar ya?
Ta bata labarin komai game da oficer,ta kuma shaida mata karo na uku kenan da yake bata bandir din dubu daddaya..na farkon da ya bani kujeru da fenti na saya,ta biyun kuma na sayi kayan sawa,nayi wa kaka itama harda waya.jiya kuma ya kawo min wata,zamu je kasuwa mu chasa shi...ko ya?
nan suka tafa,Basma kuma ta tayata farinciki,dashi ke kuma tasan relationship din dake tsakanin malama Hafsat da JUWAYRIYAN,don haka tace wa JUWAYRIYAH amman kina ganin haka yayi daidai kuwa?...ba ki tsoron bakin mutane??

Kakar dake cikin daki tanajin duk wani abu da suke fadi,ta fito tace yawwa yar'nan ki fada mata abinda take yi bai dace ba.
JUWAYRIYAH ta taba kawarta tace "keh kawalli duk abinda za'a fada,an da'de ba'a fadeshi ba...wallahi maganar mutane ba abinda ke hanani sukuni bace,idan sun so duk  inda nabi su nunani ba damuwata bace.
kaka ta sami guri ta zauna tana kallon sarautan ALLah da kuma mamakin jikarta.

JUWAYRIYAH ta cigaba da fadin"🤨😏kehh...idan bakiyi kwace ba yanzun,miji zai gagareki ki mutu ba aure.
nan ma kakar ta sake sako masu baki.."Toh sai  ki rasa wace zaki kwace wa miji sai wacce ta kawo wa rayuwarki haske?,ta farfado dake daga rayuwan kunci da yunwa!
Nan ta bata rai tace "nifa kaka ina ganin alaman baki son bani goyon baya a wannan al'amarin,idan bazakiyi supporting dina ba toh ki kau da kai..ita kuma anty hafsat da kike ikirarin kawowa rayuwata haske"fine",ai ban musa ba,idan tagan cewan ba'ayi mata dai dai ba domin taimakon,sai ta fada na biyata daga shekaru goma da suka shude....
KU biyoni a next and last page,da shike short story ne amman ful version dinsa zai zo inn'shaa'Allah..Assalamu alaikum.

2 comments:

  1. Sannu Kowa,
    Sunana Mista, Rugare Sim. Ina zaune a Holland kuma ni mai farin ciki ne yau? kuma na gaya wa kaina cewa duk wani mai ba da bashi wanda zai tseratar da ni da iyalina daga mummunan halinmu, zan koma ga duk mutumin da ke neman bashi a kansa, ya ba ni farin ciki a gare ni da iyalina, na kasance ina buƙatar aro na € 300,000.00 don fara rayuwata gaba daya kamar ni uba daya ne da yara 2 Na hadu da wannan mai gaskiya kuma Allah yana tsoron mai bada rancen da zai taimake ni da rancen € 300,000.00, shi mutum ne mai tsoron Allah, idan kana bukatar aro Kuma za ku biya bashin don Allah ku kira shi ku gaya masa cewa (Mr, Rugare Sim) yana nuna muku shi. Tuntuɓi Mista, Mohamed Careen ta imel: (arabloanfirmserves@gmail.com)


    MAGANAR BAYANIN AIKIN LATSA
    Sunan rana......
    Suna na tsakiya .....
    2) Jinsi: .........
    3) Bukatar Lamuni: .........
    4) Tsawon Lamuni: .........
    5) Kasa: .........
    6) Adireshin Gida: .........
    7) Lambar Waya: .........
    8) Adireshin Imel ..........
    9) Gashi na wata-wata: …………… ..
    10) Aiki: ...........................
    11) Wanne rukunin yanar gizo kuka kasance game da shi …………… ..
    Godiya da kuma mafi kyawun gaisuwa.
    Email arabloanfirmserves@gmail.com

    ReplyDelete
  2. This comment has been removed by a blog administrator.

    ReplyDelete

Designed by Jide Ogunsanya.