Pages

Sunday 24 September 2017

SOYAYYAR MU👫.


          By Ganarious.
13
A sanyaye nake komai tun bayan tafiyarsu Malam Lamido.
Da zarar na zauna sai na fara tunanin dan fillo.wata sa'in na shiga dakin da suka sauka nayi zaune ina tunano fuskar sa da murmushinsa ni karan kaina na kasa gane me ke damuna.
Mahaifiyata kuwa har tambayata take wai ko lafiya.! Ko so kike ki koma rugga.
Yan gidanmu sun samin suna wai "yar rugga"

       **      **      **
A makaranta kuwa dalibai,har malamai murna  ganina suke.soyayya da shakuwa ta kara shiga tsakanina dasu.
Su hafsat kuwa koransu akayi bayan anbasu ponishment.

 Akwana a tashi ba wuya gun Allah har munyi hutu.kwanarmu tara dayin hutu muna zaune a falon Babana muna hira dashi sai nake tanbayarshi yaushe za'a gama titin zuwa ruggansu dan fillo.
Yace ai jiya suka gama.
Cikin jin dadi nace Baba zan so naje gani kuwa.na lura ransa baiso ba amman ya daure yace toh ba damuwa zan sa akaiki ki gani.
  Naji dadi sosai har mahaifiyata ta lura da hakan tana fadin rabon da tagan ni cikin farinciki irin wannan tun kafin na bace.
Babana yaso daya daga cikin yannena yakaini,sai dai ba halin haka don wasun suna ketare,saurasu kuma aiki yasa su gaba.
Malam iro direba baba yasa ya kaini,dayake dashi ake ta zuwa ruggan sa'anda ake aikin titin.
Salamatu ce yar rakiya.Salamatu diyar kanwan Babana ce.shekarar mu daya kuma shakuwa sosai ce a tsakaninmu.
Babana ya umurci direba cewa a ranar zamu je kuma a ranar zamu dawo.
Tun a cikin mota farin cikina ya bayyana,Salamutu kuwa sai zolayyata take.

Mun samu kyakyawan tarbo, sai murnan zuwa na sukeyi.su Bintu kuwa ba'a cewa komai.
Munyi hira na kuma raba masu tsaraba sai dai tunda na isa ban hada ido da dan fillo ba,sunce ya fita tunda safe kuma sai bayan mangariba zai dawo.
A gaskiya zuciyata ta dan sosu,sai nake ganin toh miye amfanin zuwata.!
Karfe uku saura direba ya aiko mu fito mu tafi.Salamatu tayi saurin tashi tafice dama tunda muka iso bata saki jiki ba tana fita nayikiran ibrahim,shima kanin fillo ne.na tambayeshi ko ya san inda Buba fillo yake zuwa kiwo?yace min eh yasani.
Nace toh rakani na ganshi.bayan ruggansu muka bi ta inda malam iro ba zai ganmu ba.
   Tafiya mukeyi cikin daji har na kai ga cewa mun kusa kuwa sabida nisan gurin.yace an kusa.
  Daga nesa na hangi fillo zaune yana wasa da dan kara dake rike a hannunsa,gefensa kuwa shanayensa ne.cikin da'ga murya na kira shi.
An kuwa yi sa'a,kira daya ya juyo yana ganina yayi wurgi da karan dake hannunsa ya sheko a guje...
Ya na isowa gun da muke tsaye sai yace daga ina kika fito?yana me mamakin ganina.
nace mashi daga gida.
Murna gun fillo ba'acewa komai,sai fadin yake naji kewanki sosai...
Nace mashi ai na fika jin kewa tunda gashi na biyo ka.

Guri muka samu muka zauna muna hira.ya ce da ibrahim ya karasa gun shanayen ya dubasu.
A cikin hiranmu yake fadin da so samu ne,shi yafison ya dinga gani na kullum idan yatashi barshi.nace mashi nima haka.
Hiran fillo duk bai wuci yanda za'ayi ya rinka ganina ba.
Na kawo shawaran ko zai dawo birni ne da zama.
  "Yace wa nasania birni"
Na murmusa tare da fadin kada ka samu damuwa,kai dai kawai ka zo gidanmu zan sanar da Babana.
yayi shiru na dan lokaci sa'anan daga baya yace iyayensa bazasu yarda ba.
Cikin kwantar da murya da lallashi nace ka gwada fadamasu dai.

Sai da gari ya fara duhu sa'anan na tuna ai fa yau zamu wuce,cikin salati tare da saurin mikewa na tashi tsaye.shima ya mike ya tambayata lafiya.
yau fa zamu koma nace dashi.
yau zaku koma ina?ya tambaya
Gida,can kaduna
Tabdijam...sai dai gobe kuma.
Tare muka koma ruggansu da ibrahim da kuma shanayen.
tsatsaye muka isko mutanen gidansu tareda direba sai yayyafin masifa yakai.suna ganinmu kuwa sukayo kanmu,ana tambayata ina na shiga suna nema na.
Jin dalilin ficewata yasa direba ya kara fusata yana yarfa min masifa.
Malam iro masifaffen mutum ne,tunda na bude ido na ganshi a gidanmu yana aikin direba,yannena har kannena kai duk wanda yayi mashi ba daidai ba sai ya sha da shi.
yace yanzun dole sai gobe kenan zamu koma.
         **      **       **
Har cikin raina na jidadin haka da ya fada amma ban nuna ba.Salamatu kuwa sai hararata takeyi,bayan kowa ya watse salamatu ta fara yarfamin nata masifar wai ita yaya za'ayi ta kwana a wannan gurin.Hankuri kawai nake bata sabida nasan nayi mata ba daidai ba.
 Dakin Bintu muka sauka,muna shirin kwanciya,araina kuwa tunanin fillo nakeyi.mun kwanta kenan Ibrahim ya shigo wai buba fillo na jirana a waje.cikin murna na tashi ina fadin 'ina zuwa salamatu'
Da karfinta ta rikomin kafata,tana fadin"wai ni bangane maki ba"
Na juyo nace mata na me fa!
Nagan tunda muka zo sai wani rawar jiki kike,kina wani murna da annashuwa.
murmushi nayi batare da nayi amsa ba...ta kara fadin wai miye tsakaninki da wannan yaron mai aikowa ki fito?kun dawo tare dazun,yanzun kuma ya aiko wai ki zo yana waje.
kar ki damu idan na dawo zan fadamaki komai.
Kuttah tayi sa'anan ta sakemin kafa.
Hira sosai mukayi sai da Baban fillo ya fito fitsari ya hangemu yace dare yayi nisa,mu tashi muje mukwanta.
Na iske Salamatu tayi nisa da bacci,nima guri na samu kusa da ita nayi addu'o'i sa'anan na kwanta

Washegari bayan mun idar da sallah asubahi Salamatu ta fita waje gun mota,daman direba cikin mota ya kwana.duk yan ruggan anfito rakiyanmu harda mutan gidan malam Lamido.muna tsaye dan fillo ya matso kusa dani,murya kasa kasa yace idan nazo birni iyayenki zasu bari muyi aure?.
bazan iya kammanta maku yanda naji ba da fillo yayi wannan furucin.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.