Pages

Sunday 24 September 2017

SOYAYYAR MU

         By Ganarious.
11
A rugga kuwa bani da wata damuwa da ta wuce nagan iyaye na,Idan da sabo toh na saba dasu.na koya masu ayyuka dayawa,na kuma koyi wasu ababen a gunsu.haka nayi rayuwa a cikinsu har Allah ya kawo wani da zai je birni.
  Ana gobe zamu tafi,mukayita hiran bankwana dasu na kuma yi masu alkawarin sake dawowa.a hiranmu nake cewa Bintu idan ta haihu zan raini dan,na kuma kai shi birni.taji dadi sosai don a rayuwarta ba abinda ke mata dadi kamar ayi zancen birni,ko a cemata yar birni.

            **   **    **
Washegari na shirya tsaf duk da ba wani shiri bane.tunda nazo garin riga daya nake sawa shi din sake sakawa kuma.ina jiran mutumin da zan bi zuwa birnin sai ga malam Lamido yace tare zamu tafi don ya tabbatar na isa hannun iyayena.naji dadi sosai hakan yasa nace 'ko shi ma Buba zai rakani?
Toh...idan zashi je ba damuwa.
 Buba fillo yaji dadi sosai yace dama yana tunani dubara da zaiyi ya samu ya rakani.
Duk wani fake cikin jakkata na ra'bar masu,diary na kawai na rike a hannu..
Bintu tare da kannen fillo mata sunyi mana rakiya har sai da muka kusan fita a ruggansu,sa'anan malam Lamido yace su koma.Da kyar Bintu ta sake ni tana kuka wai baza ta sake ganina ba.nan na sake daukan mata alkawarin dawowa inn shaa Allah.
   Tafiya tayi tafiya...idan munyi tafiya me nisa malam Lamido ya kance mu huta sabida ni.da yammaci muka shiga wata kauye,a tashar kauyen muka sami motar yola don haka a hanzarce muka shiga.da daddare muka isa yola,ba kuma motar kaduna.malam Lamido ne ya yanke shawaran mu kwana a tasha da safe sai mu karasa.
  Farin cikina ya bayyana a fili,sai nake ganin kamar motan bata sauri ,kamar na fi'ra kawai nakeji..ashe fillo na lura da yanayi ya kuwa tsira min ido muna hada ido nayi mashi murmushi,shima din murmushin ya maida min.
  Da gudu na shiga gida,kai tsaye falon babana na nufa babu ko sallama na fa'da jikinsa na kankameshi da karfi,daga shi har abokansa dake falon sun tsorota don kuwa ba wanda ya gan fuska ta a cikin su kuma ban fuskance su ba.Babana kuwa kokari kawai yakai ya banbaroni daga jikinsa yagan fuskan waye amman ina....sai kuma ya koma yana fadin wacece ke?
Sai da naji abokansa na fadi a kira masu gadi sa'anan na sake shi..muna hada ido kuwa yayi kabbara tare da sake rungume.
Babana kenan....mamee na kaiwa nan ta kalli ilham da Hisham da suka tsura mata ido,ita kadai suke sauraro,sai ilham kam ido yayi jajir tana kara tausaya mameen ta.
     **      **       **
Cikin share hawaye da ya dan taru a idon mamee ta chigaba da fadin' Babana na so na sosai'..komai nake so,shi yake so.idan nace A,toh A zai zama a gidanmu,idan kuwa nace B toh B ne sai dai haka be sa na shashance ba don na taso da natsuwa da sanin ya kamata.
Baba na yana rungume da ni cikin farin ciki da anashuwa,idan ya sake ya kalli fuskata sai ya rungume ni,can kuma ya sake kallona ya rungumo ni yana fadin Aisha kece? Haka dai ya rinka yi kamar ance za'a sace ni..Abokansa ne suka taso suna tanbayata abinda ya faru.
nan na fada masu komai daga farko har izzuwa wannan lokacin,sai lokacin na tuno ai tare muke da su malam Lamido.Da sauri na fito,shima babana ya biyoni.ko da muka isa,mun iske su Malam Lamido zasu tafi don kuwa me gadi ya hanasu shigowa.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.