Pages

Thursday 27 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
    By Ganarious.
8⃣
Bayan na bude takardan sai na gan rubutu kamar haka.'hahah..idan har kin tashi kin gan wannan takardar toh ki godewa Allah..ba mu sonki,bamu kuma kaunar ganinki.shiyasa mukayi maki hakan.sai mun hadu a can.
  Sai a wannan lokacin na tuna abinda su hafsat sukayi min.kuka na shiga yi sosai ina fadin menayi suka tsaneni haka!
Fillo kuwa ba abinda ya kai sai kallo na...sai da nayi me isata sa'anan nayi shiru domin kuwa kaina ya fara saramin,kamar jira yake nayi shiru sai yace min na tashi mu tafi tare da yimin addu'a da fulfude wai Allah reene,Allah seyne!.
   Tafiya mukayi sosai sa'anan muka isa ruggan su.yan uwansa sunyi mamakin ganin fillo tare da dani,sai na zama masu abin kallo.
Da fillatanci yayiwa iyayenshi bayani.
Na dade tsaye don kuwa dan fillo da yan uwanshi gabaki daya suka shige wani daki sai wasu kananan yara da suka firfitoo suna kallona kamar sun gan wata halitta.har na fara jin haushin biyoshi danayi.ina a tsayen,sai gasu sun fito amman kuma basu cemin komai ba,ko ga guri zauna ma ban samu ba...shima din fillo haka yazo ya wuce ni bai ce komai ba...hankalina duk yatashi ina tunanin me mutanen nan ke shirin yi dani.
 Guri na samu na dan tsuguna,ba abinda nake tunani sai sallolin da Ke kaina..ina cikin wannan tunani na hangi wata budurwa zatayi sa'ata a girman jiki,amman a shekaru mu ba tsara bane.itama din dai kallona takeyi har tana tuntube,da hannu nayi mata alama da tazo."don Allah ina zanyi fitsari?"nace da ita.
Bata amsa ba sai kallona takeyi na sake yi mata magana nan ma bata amsa ba ta juya ta wuce abinta,..gashi fitsari ya matseni sosai.
Nabkoma na tsuguna ina tunanin wannan wata rin rayuwa ce...sai kawai kuka ya zo min...amman kuma mutanen kamar dabbobi sai kallona sukai daga ne'sa.
   Kuka fa nake sosai,sai ga dan filli ya dawo shi da wani mutum.suna isowa na mike sauri nace fitsari nake ji wannan mutumin yace a kaini bayan ruggansu nayi fitsari   sa'anan na dawo.
Wannan mutumin dogone me kyan gaske gashi fari tas dashi,sai kuma Allah ya bashi abinda mata ke kira dimple...ya tambayeni duk wani abu da yake son sani game da haduwata da dan fillo kuma da dalilin da yasa aka bar ni a daji..na kuwa fada mashi komai da komai daga kan abinda su hafsat sukayi min har yanda muka hadu da dan fillo.na kuma rokeshi da ya taimaka min na koma gun iyayen A kaduna.
'toh naji zamu taimaka maki mu maida ki gun iyayenki sai dai ba wanda zai je birni cikin yan ruggan nan.amma idan ansamu za'a mai dake gida.
Shiru nayi ina me rokon Allah a zuciyata da yakawo min mafita.

Wani daki suka kaini wai nan zan dinga kwana,da kamar nace masu bazan iya kwana anan ba amma ba yanda zanyi dole na na shiga ciki a takure na zauna.
A sannu sannu na fara sabawa dasu sai fai wasun su ba su jin hausa sai fulfude...Na rame sosai don kuwa tunda na shiga ruggan bana iyacin abincisu duk da kokarin danakeyi na turtusa kai na amman abin ya ki don kuwa idan na tursa kaina to amai ne zai biyo baya,hakan asa iyayen fillo cewa a dinga ta'cemin nono shanaye.
  Nafi shakuwa da dan fillo,idan za shi kiwo sai na bishi idan har ba zai dade bane.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.