RIKICHI
Episode 5
By Aisha Gana(Ganarious).
Ita dai wannan baiwar Allah yar' kasar Maxico ce. Mahaifinta Muhammad Ali shine dan asalin maxico, mahaifiyar ta kuwa yar' kasar yamen ce.
Su biyu kacal iyayen ta suka haifa, ita ce babba sai kaninta. Mahaifinta Ambasador ne na maxico zuwa Nigeria. (A shekarun baya.)
Da farko iyayenta basu yi marhaba da zancen ba, amma da shike basu son bacin ran ta, haka yasa don dolen su suka amince.
Bayan auren Hafsat da mahaifin mu, wasu kofofin arziki suka budewa mahaifin mu, arzikinsa ya bunkasa na ban mamaki shi kan sa tsoro ya kan kamashi idan ya duba ya gani.
A wannan shekarat mutanen gomasha bakwai mahaifin mu ya biyawa aikin hajji. Ya yi gine-ginen shaguna da gidaje ya baiwa wasu kyauta, sannan kuma an saka yan haya.
Tun da sukayi aure bata taba zuwa garin mahaifin mu ba, sai da tayi shekara daya da watanni uku, alokacin tana da shigen ciki... Sai dai daga ita har mahaifin mu babu wanda ya sani.
Yan uwan mahaifinmu sunyi farin cikin ganinta, mutanen gari kuwa sai tururin zuwa ganin baturiya sukai.
Satin su biyu suka koma.
Sunyi murna sosai sa'anda aka sanar masu Hafsat na dauke da ciki. Basu da wani buri da ya wuci su gan ranar haihuwa da kuma dan da zata haifa... Yau ma kamar kulum, tana zaune da mahaifin mu "ya ce Boy or girl" da shike haka suke yi kulum!
Kai ma kasan Boy nake ra'ayi ai, tayi murmushi hade da jan kuncinsa! Duk wanda Allah ya kawo ina son..
Shima Mahaifin mu ya murmusa yana me mata kollon so da kauna.
Ta sake duban sa ta ce ka san me?
A'a sai kin fada ya maida mata.
Idan har Boy din na haifa, ina neman alfarma da a sanya masa suna SAMEER.
Na Amince, amman sai kin fada mu dalili.
Ta numfasa, tare da gyara zama sa'anan sa soma bashi labari. "tun muna yara jinin mu ya hadu. Watau da Sameer . Mun shaku sosai. Sameer dai dan makwabcin mu ne shi, mahaifinsa shima Ambasadon Jidda ne zuwa Nigeria.
A tare muke zuwa makaranta, komai tare mukeyi kamar su Assignment da sauransu. A lokacin ni kadai ce iyayena suka haifa, shi kuma a gidan su su biyu ne.
Sameer uztazu ne sosai, ko mahaifiyarsa tayi ba daidai ba, sai ya ce "Allah ya hani kaza da kaza"
Shakuwar mu ta kai ga har idan muka yi hutu, sai mu je kasar mu tare, wani hutun mu je nasu. Ba ka ta ba jin fadar mu, sai akan rashin daura dankwali. A cikin hirarakin mu sai ya ce idan matar sa ta haifa masa ya' mace sai ya sanya mata suna na, ni ma nace masa zan sanyawa da' na Sameer.
Ranar wata alhamis, na tashi da rashin kwarin jiki sakamakon mafarkin da nayi. A mafarkin wai Sameer ne sanye da fararen kaya, sai murmushi yakeyi, na maida masa hade da fadin wannan murmushin fa? " ya shafe kaina, hade da bude baki zaiyi magana sai wata katuwar tsuntsuwa ta dauke shi... Ihu nake, ina kiran sunarsa, ga shi wai cikin jeji ne, ni kadai ke jejin tsoro duk ya mamaye ni, ina me ihun kiran sunan sa.... Firgigit! Na mike, jiki na sharkaf da zufa. Nan nayi zaune ina me mamakin wannan mafarkin.
No comments:
Post a Comment