Pages

Sunday 29 December 2019

SOYAYYAR MU👫 58

SOYAYYAR MU👫🏻

      || Page 58 ||

By Aisha Gana (Ganarious)


Assalamu Alaikum Readers of Soyayyar mu!
Trust you are doing good. I'm so sorry for not continuing/updating you guys with the story.
By Allah's will, i will continue from where i stopped.
But! I really love to hear from you. If you can't drop your comment here, you can send your view to ganarious98@gmail.com
Thank🤗.

     *       *        *         *
Bayan da Dr. Abdul'Afeez ya tsawatar wa ilham, ya kuma kafa mata doka cewan kullum tazo tayi signing a gun sa, sabida ya tabbatar ta zo din.
    Hakan ya farantawa Hisham rai, ya jidadi sosai, ko babu komai zata chigaba da karatunta.
Ba shi kadai ba, har kawayenta, da Nura da abokansa kowa yayi farin ciki da haka. A yayinda ita kuwa ranta yayi baki. Ta raya a ran ta cewan ai kuwa Dr. Abdul'Afeez bai isa ya sanya ta abinda bata yi niya ba. Don haka baza ta je din ba, sai dai yayi duk abinda zai yi.
Washe gari su yusrah sun kammala shiri, ita kadai ce suke jira, wankan ma ta ki yi balle ta sanya kaya, nan suka shiga yimata magana,suna roko da lallashin ta, amman ta ki sauraron su!
Haka lectures din ranar ya wuce su, sabida ita, suma suka ki zuwa. Tou amma abin godiya shine a ranar ba ta da course din Dr.
          *    *     *        *
Tun bayan Sallar Asubahi, yake cikin Anashuwa, kallo daya zakayi masa ka fahimci hakan.
Sky blue shadda wanda ya sha aiki da dark blue zare ya ciro ya sa, bayan ya yi wanka ya bi ilahirin jikinsa da Arab oil perfume.
Abokan sa na ganin haka, suka soma zolayar sa. " yau fa zaka rudar da ya'yan turawa", kana sane wannan shirin naka na rudar da su.
Murmushi yayi ba tare da ya maida masu maganar ba.
Manya kayan al'adar malam bahaushe yana yiwa Hisham kyau sosai idan ya saka, duk ranar da zai saka su sai ka gan yan'mata har maza suna zu gunsa suna daukan hoto da shi.
 Bangaren su ilham kuwa, tun bayan sallar asubahi din, su Naziha suka shiga damuwa, suna shaku kar ilham tace baza je lectures din ba.
Haka kuwa ta faru! Ganin lokaci na kurewa bata shirya ba ya sanya su sanya ta a gaba, suna mita "Haba ilham, please don't do this.
Kallon su matayi ba, a fusace Amarah ta mike "tou ku tashi mu tafi, tunda dai ta nuna babu mahalukin da ya isa da ita"....
Duk jikin su yayi sanyi, hakan ya sa yusrah ta dafa kafadar ta "Haba ilham! Allah ma fa anai masa mafi munin laifufuka kuma da zarar ka roke shi zai yafe maka, balle mu.. Wannan abun fa kan ki kike cutarwa ba wani ba, kin sawa kanki damuwa, kin ki zuwa lectures gashi kina son ki batawa kanki suna gun malamin ki, don Allah ki manta da komai mu cigaba da rayuwar mu kamar da.
Kuka ta somayi! Nan suka shiga lallashin ta, sai da tayi me isar ta, sa'anan suka taimaka mata tayi wanka, ta fito sannan suka nufi cikin makarantar.
Tunda ya soma lectures ya ke duban hanya ko zata shigo, gashi har ya kusan gamawa bata iso ba, hakan ya sosa masa rai...
Yana matakin maimaita abinda ya koyar, ta shigo!
Ajiyar zuciya yayi, sai kawai ya tsinci kansa da farin ciki. Nan ya shiga maimaita duk abinda ya koyar har sai da wani malamin ya shigo.
   Itace ta farko da ta fara barin ajin, sa'anan sauran daliban.
A hanzarce ya fito shima, yana waige waige ko zai gan ta. Cikin nasara kuwa ya hange ta jingine da wani icce, don haka ya nufi gurin.
Da sallamar sa ya isa gurin, ta juyo ta dube shi ba tare da ta amsa ba! "How are you doing Aisha?" ya fada yana me kallon fuskarta
Ta dube shi sukayi ido hudu, sai ta dago ta tofa masa yawu!
A hankali ya sa tafin hannunsa ya goge. Ya sake duban cikin murmusawa yace.... Idan har hakan zai sa ki huce  ki yafe min, a shirye nake da amsan hakan, please.
Bata dube shi ba balle ta tamka masa, nan ya shiga bata hakuri..i'm so sorry Aisha.
Bai ankara ba ya ji kukan ta... Subhanalillah, har cikin ransa ya ke jin wannan kukan nata, ya rasa shin rungume ta zai yi ko me...
Cikin rudewa ya shiga bata hakuri, yanzun kam da karfi take kukan, duk masu wucewa sai kallon su keyi.
Suna a haka, Nura da tawagar sa suka iso! Shi din ma a rude ya karasa gab da ita da niyar ya rungu me ta, hannu ta sa ta ture shi.
A hasale ya karasa gaban Hisham "You son of bich" yana fadin haka yasa hanu ya ture shi a kirji. Ya kuma sake matsawa kusa da shi zai kai mashi duka Hisham ya rike hannunsa gam! "don't try that! I'll smash you" ya fada tare da ture masa hannun nan abokan Nura suka yo kansa ga baki dayansu suka shiga dukan sa!
Ganin su duka shi kadai ya sanya ilham shigowa tsakiyar su tana kokarin raba fadan, amma ko sauraronta basu yi ba, sai fadin take "Enough" "Enough"!! Enough of this! Duk da haka basu daina ba sai da masu kai da komawa suka raba fadan.
Kashe gari ma, sai da ya kusan gama lectures ta iso. Amman yau bai sami damar maimaici ba, sabida wani malamin zai shigan masu, kuma shi din ma yana da lecture.
Don haka bayan lectures bai sami ganin ta ba.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.