Pages

Friday 13 December 2019

RIKICHI 1

RIKICHI

 Bismillahir rahmanir rahim.

Da sauri da sauri ta ke tafiyar, wanda dayawan mutane da basu san ta ba, su ke dauka salo da yanga ce.

  Marhaba da isowa gimbiya ranki shi dade.... Wata murya ta fada hade da fadin "karaso ciki mana"

Ah'ah sauri nake, gobe idan da rai da lafiya zan dawo.

Ki shigo mana, idan na karasa wankewa wannan sai na wanke maki?

Ban tsaya sauraronta ba, nayi tafiya ta. Jiran nake motoci da su adaidata sahu su tsakaita na tsallaka zuwa dayan gefen titi. Sai faman waige waige nake ina mai kallon hagu da dama ta, ban ankara ba sai jin nayi an taba  min kafadata.
A firgice na waiga. Hade da fadin subhanalillah! Nan ta ke na shiga yiwa Allah tasbihi.
Kallon kallon muke yi a yayinda ababe da dama suke ta aukuwa a zuciya ta "yau kam nayi gamo da aljana"
   Maganar ta ce ta farfado da ni. "i m very sorry, bani masaniyar zaki tsorota haka, tun da kika fito daga saloon din nake maki sallama, amma da kamar baki ji ni ba, shi yasa na biyo ki
 Ba komai, na fada hade da yin ajiyar zuci.
  Ta nisa, sa'anan ta dube ni cikin ido "taimako nake son kiyi mun"
Cike da mamaki nace 'taimako?

Ta daga kai' alamar eh kenan
Cike da mamaki nake kallonta, sabida batayi kama da wace ke neman taimako ko wace iri bace. "wace irin taimako kenan?  Na nemi sani.

Mmhhh.... Ban san daga inda zan faro maki ba, amma ina ganin sai na baki labarin kaina tukun sa'anan zaki fahimce ni.
Na dubi agogon hannuna, sannan na dube ta yanzun dai ina kan hanyata ne, amman ga lambar wayata da addireshi na, sai ki neme ni. Tayi godiya sa'anan mukayi sallama.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.