Pages

Tuesday 3 July 2018

Page49 of SOYAYYAR MU

SOYAYYAR MU👫
      By Ganarious.
4⃣9⃣


         **        **          **
A tare suka ficce da'ga hall din,sai dai shi wannan gayen  na gaba gare ta, ita kuma tana biye dashi.
 Tsaye sukayi bayam sun fito da'ga hall din.a yayinda shi ya jin gina jikinsa ga bango.

Kai da komowa ilham takeyi, tana me jin haushin abinda ya faru. Ranta ya kara ba'ci fiye da ta baya...ganin take yi kamar ma dan renin hankali ne.
Don haka ta nufe shi a harzuke, bai ankara ba yaji an taka masa kafa.
Da karfin ta kuwa ta take kafar, kamar yanda ake takan kwaro.

Da'ga kafar yayi, yana fadin ...."wash, wasshh....
Dubanta yake yi bayan da zafin ya dan lafa....ita ma shi take kallo, a ranta kuwa kamar ta kamashi da duka take ji.

Matsowa yayi gab da ita tare da da'ga hannunsa zai kai mata naushi.....ji an rike masa hannu ya sanya shi juyawa don ganin wa ne ne.

Nura ne tsaye, sai huci yakai, yana da'ga kirji sama, yana maidawa kasa....."Allah ne ya taimake ka,da yau ka gwammaci mutuwarka"

Ya fisge hannunsa tare da juyawa suka fuskanci juna da Nuran.
Ya kai yatsansa kirjin nura, yana me nunashi...."na sha fada maka,bazan ta'ba bata lokaci na fuskance ka ba,,har sai randa ka girma,don haka get out of my sight"
Yana rufe baki, abokan Nura wadanda suke tafiya atare suka iso gurin...nan suka zagaye wannan gayen wanda a lokacin ban san sunansa ba.

Nan da man jikina ya soma rawar sanyi,tsoro ya ziyarci zuciya ta, domin kuwa abinda nake kallo a fims din turawa na shirin gabatuwa a gabana,kuma a dalilina....a'a a'a na fada ina me girgiza kai tare da shigewa tsakiyarsu.
"get back to ur senses,i never ask any one of you to assist or fight for me,ta matsa gun nura...."ce masu su watse"
Da idon sa yayi masu alama, nan ko wannensu ya kama gabansa.

Rike masa hannu tayi..."lets go ta fada, a yayinda suka soma tafiya.
Wannan gayen da bata san sunar sa ba a lokacin, ya zo ya sha gaban su, a yayinda suka dakata suna duban sa.
'"wannan ya nuna kai yaro ne har yanzun"
Ya juya ga ilham yana nuna ta da yatsa..
Kafin duk a soma magana, ta sa hannu ta buge masa yatsan.

Murmushi yayi...."da alama ke sabuwa zuwa ce ko? Toh ki sani,wannan makaranta zai ya fi maki wuta zafi,don haka ina me baki shawaran da ki nemawa kanki sauki ki bar wannan makaranta tun gari baiyi duhu ba.
.
ta saki hannun nuran tare da takowa gab da gab dashi, domin kuwa tana shakan numfashinsa.
Duban fuskansa tayi,ta kai kanta kasa ta dubi fuskarsa....sannan ta da'ga kafarta sama ta take masa kafa kamar yanda tayi a baya....."shege ka fasa,idan ni ban gudu a wannan makarantan ba, kai zaka gudu da wadannan kafafun naka.

Fuska a murtuke yake kallonta,cike da mamakin wannan wace irin yarinya ce.

Nan ta sake rikewa nura hannu..."lets go" ta fada..

       **      **    **
Su naziha harda cizon yatsa tana fadin kash.... A lokacin da ilham ke labarta mata abinda da ya faru tsakaninta da wannan gayen.

      Duk ranar asabar dalibai musulmai ta makarantan kings college suke gabatar da taronsu ta muhawara da karuwa da junansu a musulunci.
10:00am suke haduwa a babban dakin makarantan domin yi m.s.a.o activities na su.
An wayi gari,asabar....9:00am shine lokacin da masu mukami a m.s.a.o suke zuwa gurin da ake taron domin ganin komai, daga kan share share zuwa kan jera kujeru sunyi dai dai.
10:00am shine a ke soma activities din.

Ilham tana daya daga cikin masu zuwa gurin tun 9:00am, ba don tana da mukami ba, sai don ganin ta kama masu aiki da arrangement din gurin.
Ilham ta tashi da kasala,har ta yanke cewan zata hakura da m.s.a.o Din ranar.
Bayan su naziha sun kammala shirin su, su ka nufo dakin su ilham din, sun tarar bata shirya ba, kwance take tana operating wayarta.
Da zuwansu Amarah ta kai mata naushi..."tashi ki shirya mu tafi"

Ku tafi kawai,ni yau bazan sami damar zuwa ba.

Sabida me?,...."Amara ta fada a yayinda ta sami guri kusa da ilham din ta zauna.

Da kyar....suka shawo kanta, sa'anan ta mike ta shige toilet.

Doguwar rigace ta saka, ta fiddo wata karamar hijabi wanda zamu kiransa hijabi hade da nikab, ko mayafi ne hade da nikab.

Waw....naziha ta fada, bayan da ilham ta daura wannan nikab din a fuskar ta.

Wannan kuma yaushe ya fito?..."fadin Amarah
Mamee ta yo min tsarabar sa daga egypt..

No wonder,don da alama babu irinsa a kasuwa tukun.

Gaskiya kinyi kyau, wannan designer nikab din ma ya kara fito da ke......

Sai 11:15 suka isa gurin,a lokacin an kusan gama activities din....a lokacin da suka isa gurin wata daliba ce ke karatun al-qur'ani, don haka suka sami guri daga baya, suka zauna sabida ba guri a gaba.

Bayan da daliban ta gama karatu, me  gabatarwa da loudspeaker, yayi takbira mutan gurin suka amsa. Saanan  yace "anan muka kawo karshen masu karatu,abu na gaba shine wa'azi, wanda a yau daliba daya kawai zata gabatar sabida lokaci.
Dalibar itace Aisha b. Musdafa.

Dafe kirji ilham tayi...."oh ni ilham,ko shirya wa wannan wa'azin banyi ba,toh ni yanzun me zani yi wa'azi akai?
Tana rufe baki aka sake kiran sunan ta.

"dont worry, ke ce fa....fadin naziha a yayin da take shafa gadon bayan ta.
Mikewa ilham tayi tana takun nan  na ta,ta nufi stage din.
Sai da ta haura sama sa'anan ta gane fuskar me rike da loudspeaker yana jawabi.
A gabansa kuwa, wata kyakyawan gilash ne me dauke da suna " *AMEER* "...kallon kyau tayi masa, daman wannan din ne amir, daman da nan mutane suke fadin munyi kama...tabdijam..du a zuci take raya hakan

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.