Pages

Thursday 8 February 2018

SOYAYYARMU 34

*SOYAYYAR MU👫*
         By Ganarious.
Page 3⃣4⃣

DOMIN KI *Nazhee yareema*😃...Babban abokiyar ilham.

Labarin *KAZAMACE MATATA* na nan a ganarious.blogspot.com/
Kar ku bari a baku labari.

Gaisuwa ga masu karatun *SOYAYYARMU*,Kuyi hakuri da kurakuren da typing errors da labarin ya kunsa.🤞🏼

         **       **         **
Ya jingina jikinsa da motan.
Hajiya zubaidah ta karaso gunsa tana taba shi ya sulale kasa.
   Ta shiga cikin gida a guje tayi kiran me gadi.
Da taimakon mai gadin,suka shigar da alhaji Buba wanda yake a sume.

Yana farfadowa ya fara surutai.
Hajiya cikin damuwa take fadin 'ka kwantar da hankalinka,da yardan Allah za'a gan takardun..
Ya dube ta cikin ido,yace me kike fadi?.
Nan ta sake maimaita masa abinda ta fada.
Ajuyar zuciya yayi,ba tareda yace mata komai ba.

Karee da kaseem ne a mota.
Kaseem ne matukin,kareem ya nisa yace ya kamata mu dubo Hisham,mu san halinda yake ciki,domin kuwa saura kwana hudu kacal ilham ta aiwatar da alkawarin ta..
Hummmm....wallahi,nima abin ya dame ni.gashi duk mun kasa samun mafita...fadin kaseem.

Sun danyi shiru na lokaci,sa'anan kareem ya dubi kaseem yace 'guy kasan me?
Kaseem ya girgiza kai yace sai ka fada.

Juya motan mu je gidan Hisham.
Ba gardama kuwa ya yi rivas suka kama hanyar gidan Hisham.
Yau ma a kwance suka tarar da shi.
Yayi masu barka da zuwa.
Bayan sun zazzauna kareem ke fadi"ya ya ake ciki ne aboki?..ko ka sami mafita? Don lokaci na gabatowa.

🤦🏻‍♂da'fe kai yayi "wallahi har yanzun ban sami mafita ba....kwakwalwata ta daina aikin ma.
Dariya suka yi masa.

A gani na kuma idan za'a dauki shawarata,muje gurin mamarta kawai...muyi mata bayani daya bayan daya akan abinda ilham din take shirin aikatawa.
Itace kawai zata iya hana ta.
Duk sun amince da shawaran kaseem,amman Hisham na me kwankwonto akan mamee baza ta amince da maganarsu ba.

Gidansu ilham suka nufa,me gadi ya sanar da su mamee tana gurun aiki, basu fidda rai ba suka nufi guri aikin ta.
Sunyi dace domin kuwa ta fito lectures kenan,tayi masu izini da su shiga offishinta ita ma din tana biye da su.
Baby Muhammad,(Abba) ne zaune yana buga games a laptop dinta,yana jin motsin shigowarta ya nufe ta yana fadin "wani lokaci ne zamu je sanyan ice cream din,a shagwabe yake maganar kamar zaya yi kuka.
Rungumeshi tayi,ta sumbaci goshinsa'yanzun nan,baba na...amman sai  ba'ki sun tafi tukun.
Sai a lokacin ya dubi su hisham tare da risinar da kai yana gaida su.
Bayan an natsu mamee take tambayarsu abinda ke tafe dasu.
   Kaseem ne ya wakilce sa da yin bayanai akan abinda ke ta'fe dasu game da ilham.

     Dariya sosai mamee tayi sa'anan tace "kuma ku dauki maganar ta muhimmaci?...toh ku kwantar da hankalinku sabida ba abinda ilham zata iya yi...besides akan wani laifi zata sa akamasu?🤷🏻‍♀..babu! Don haka ku kwantar da hankalinku,ku daina tunani irin nata.
    Nan mamee ta shiga jadada masu akan ilham bazatayi komai ba,bacin rai ne yake sanyata fadin haka.

Sunyi godiya tare da mike wa don kimawa inda suka fito.
Hisham ya mikawa Abba hannu yana fadin 'ka bini mana,na saya maka ice-cream din tunda mamee na aiki yanzun.
Cikin jin dadi yace'toh'...ya juya ya dubu mamee "mamee na bi wannan uncle din?
    Ofcos! Ai yayanka ne shi.
Ya mike yana tsale tsale..cikin jin dadi yayiwa mamee sai ya dawo.

Suna fita da'ga offishin mamee wayat hisham ya shiga ruri......ganin me kiran ya sanya shi yin tsuki,tare da maida wayan cikin aljuhunsa.
Wayan tayi ringing kamar sau biyar,ganin ba'a hakura yasan zuciyarsa na raya masa watakila wani abu na faruwa ne.
ya dauki wayan,baba lamido ne.
Sun gaisa..can bangare baba lamido ya umurce shi da ya zo yanzun nan suna nemansa.
Bayan ya gama wayat yacewa kaseem 'muje gidan baba lamido,suna nema na acan....ya kai kallonsa ga Abba 'zamu dan biya wani gida,kayi hakuri..idan mun fito sai muje gun sayan ice-cream din.
Abba yayi murmushi "ba komai uncle.'

A waje sukayi parking mota...suka karasa cikin gidan da kafa.sai dai Hisham ne kadai ya shiga ciki-cikin gidan.
Kaseem da kareem harda Abban samun guri sukayi  a gurin da aka ke'be don hutawa,don haka suka zazzauna suna jiran fitowan Hisham.
Suna zaune gurin,me gadi ya wangale gate...Alhaji buba ne ya shigo,yayi parking ya fito dagacikin motan.
Gefen su ya biyo za ya shiga cikin gida,nan kareem da kaseem suka gaishe shi,ganin haka yasa Abba ya gaida shi,shima.
Har ya juya zai wuce,sai kuma yayi kiran Abba da hannu...ya mike ya nufi gun da Alhaji buba yake tsaye..
"Kai dan wani gida ne?
shiru abban yayi na dan lokaci,sa'anan yace nima ban san sunan gidan mu ba.
Alhaji buba ya murmusa,ya kai hannunsa kafadan Abba tareda risunowa 'ko zaka iya fadamin sunan babanka?
Mustapha sunan babana..ya bashi amsa a takaice.
Kai fa?..alhaji buba ya sake tambaya wa.
Ni?😳...a makaranta muhammad mustapha ake kirana,mama na kuma tana kirana Abba.
Hisham ne ya karaso gurin a lokacin da Alhaji Buba ke shirin sakeyiwa Abba tambaya.
Ya gaida shi, shima ya amsa cikin fara'a yana  me tambayan Hisham 'wannan yaron dan wani gida ne?.
Shiru hisham yayi ya rasa amsar da zai bashi....sai da alhaji Buba ya sake tambayarsa sa'anan yace  kanin ilham ne..
Da shike yasan da zacen ilham da hisham din,ya kuma san hargitson da ake ciki.
Ya dubi Abba,ya kara risuniwa ya sumbaci goshin sa.
Ya sa hannu ya shafi kuncinsa tare da fadin ya'ya kake?
lafiya lau ya maida masa.
Ya'ya yayanka mujaheed?
Lafiya lau,ya sake fadi.
toh madallah..

Yana tafiya yana waigowa,shima Abban alhaji buba yake kallo.
Hisham ya taba shi yace muje ko?
A hanyarsu ta komawa,abba ke tanbayar Hisham waye shi wanan mutumin da ya sumbace shi a goshi?
Kanin mahaifi na ne.
Murmushi yayi tare da fadin uncle Hisham zaka sake kawoni wannan gidan na gan sa?
kai ya da'ga masa 'inn shaa Allah.
Cikin jin dadi yace yes!!💪🏻,na gode uncle Hisham.
bakery din da ke unguwar sarki,suka nufa.
Ya umurci Abba da ya fadi abinda yake so,
ice-cream kawai nake so,fadin Abba.
Hisham ya saya masa ice-cream din ya kuma hada masa da cakes masu yawa...daga nan gidan hisham suka nufa.

Sai bayan ssllan magrib,ya tafi maida Abba gida.
HAR cikin gida ya shiga.
Blessing na bude masa kofa,idonsa ya kai kan gimbiyarsa tana saukowa daga sama...
mamee kuwa,na zaune a kujerun alfarma da suka kayata falon,tana me dane danen wayarta.

A GUje Abba ya isa gurinta,ya ajiye ledojin da ke hannunsa bisa teburin ya rungume mameensa yana sumbatatan.
Ya bude ledan ya ciro daya daga cikin robobin ice-cream din,ya bude ya shiga bata a baki.
Ya is a haka babana,..na gode..fadin mamee.
YA Girgiza kai 'a'a,sai kin shanye duka na cikin roban nan.
SAI da ta kakalo aman karya,sa'anan ya daina bata.
Ta dubi Hisham da ke zaune yana kallonsu tayi masa godiya.
Gimbiya kuwa ta daura kafarta daya bisa dayan...bata gaida Husham ba,balantana tayi masa magana.

"Baka yiwa anty tayin ice-cream din ba"
Cikin turo baki yace"itama bata bani nata."
toh ai na fada maka,ka barta da halinta,duk abinda tayi maka ka daina ramawa,kaji babana!.
Ilham dai sai kallonsu take,tana me takaicin abba.

Yaawaaa....kinsan me mamee!.
A'a babana,ban sani ba ssi ka fada.
da muka fita da uncle Hisham,munje wani gida na gan wani mutum me matukar kama da Anty.
idan da kana zaune kusa da hisham,zakaji hargitson da ya'yan cikinsa suke yi,sabida maganar abba ya razana su.
Cikin mamaki mamee ta kalleshi tace kohh?
eh wallahi mamee..kin ma san me?
Kai ta sake girgizawa,tana me duban fuskarsa.
Banda kamanin da suke dashi da anty,harda wannan abinda take dashi a gefen bakinta,shima yana dashi...kuma ya san ya'ya mujaheed.

Shi kadai kawai suke kallo,yana zuba masu surutu..
YA mike cikin farin ciki da anashuwa yace ..kuma kinsan me?
Kai ta girgiza.
wallahi inason mutumin nan,sabida ya sumbace ni yanda kike yimin.
Shiru mamee tayi,banda kallon Abban, ba abinda takeyi.
Dallah yiwa mutane shiru...da'ga yau na sake jin kayi maganar wannan mutumin sai na yi maka dukan tsiya..
TA DUbi Hisham a fusace tace "kai kumaa...
mamee ce ta tsinke mata maganarta.

MAMEE ta dubi Hisham tace'na gode kwarai da gaske,akan dawainiyar da kayiwa abba..sai dai kuma idan bazaka damu ba,abinda ya faru,yau bazani so ya sake faruwa ba.
hisham yayi gyaran murya,ya baiwa mamee hakuri tareda yin alkawarin hakan bta sake faruwa..
........fuuuuu ta mike,tare da barin gurin.
Mamee da dubi Hisham,tace kar ka damu da duk wani abu da zata ce maka,nima kuma zan fahimtar da ita.
A sanyaye ya bar gidan,har gun motan ss abba yayi masa rakiyah,yane me tambayarsa yaushe zai sake zuwa suje gidan.?

Ka'sa zama tayi tun da ta koma daki...sai kai da komawa take,tana me jin haushin abinda Hisham yayi a yau....tayi kuttah,tana raya wa aranta sai ta hukuntashi.

Mamee ce ta turo kofa,tana ganinta ta bata rai.
Gefen gadonta mamee ta zauna,ta riko hannunta tare da jawota ta zaunar.
"Me kike kinsawa a ranki yanzun kuma?...cikin ido mamee ke dubanta ayayin da tayi mata wannan tanbayant.
Shiru tayi bata amsa ba.
wannan bacin ran dai na san sabida abba ya hadu da mahaifinku ne ko?
Kai ta da'ga,batare da ta dubi mameen ba.

Ki sa a ranki haka Allah ya rubuto zai faru,ko ba da sanadin hisham ba,idan ma dake ne zai hadu da mahaifinsa...kuma kar ki manta jini na da matukar karfi.
Don haka bana son ki baiwa Hisham laifi akan faruwan haka....da haka mamee ta shawo kan ilham da nasihohi.

Mahaifin hajiya zubaida ne zaune da abokansa wa'anda suke shirin hada hannu da karfinsu domin sanyan kafani da aka kawo masu talla daga japan.

*FAHAD INDUSTRIES*,kamfani ne  na ke'ra motoci,mashuna,kekuna da duk wani abu da ya shafi karfe..me wannan kamfanin ABDULRAHMAN IBN FAHAD balarabe ne daga kasar saudiyah.shine mutumi na uku a jerin masu arzikin a kasashen larabawa..a jerin masu kudin duniya kuwa shine na goma shabiyu.
 Dan wannan balaraben me suna Fahad shine ya kawo wa mahaifin hajiya zubaida tallan kamfanin.
ya sanar mashi cewan mahaifinsa ya rasu ne kason sa kean wannan kanfanin shiyasa yake son ya saidashi.
ganin wannan garabasan ba tareda wani tunani ko nazari ba, ya sanya mahaifin haj.zubaida kiran abokansa,domin kuwa bashi da kudin da zai iya saya masa kamfanin...asalima duk fadin africa,ba wanda zai iya sayan sa shi kadai,komai kudin sa kuwa.

  Abokan mahaifin haj.zubaida sunyi mamakin jin rasuwan Abdulrahman ibn Fahad da'ga sama sabida basu ji rahotani a news ba ko a social media.
Suma din basuyi bincike ba suka aminta da tayin mahaifin hajiya zubaida don haka suka fara dabaru da kuma kudin da ko waninsu zaya bada..
sun nemi da akawo masu samples da hotunan kanfanin,yaron yace masu su turo daya daga cikin su ya zama masu ido,ma'ana ya dudduba masu kanfanin.

a cikin sati daya akayi komai da komai,umurnin yaron kenan.sabida ya shaida masu idan suka wuci sati dayan zai fasa saida masu.
hakan yasa mahaifin haj. Zubaida ya tattara makudan kudade har biliyan hudu,ya turawa fahad,dalili kenan da aka kawo takardu,suka fada a hannun Alhaji Buba.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.