Pages

Monday 5 February 2018

Page3 OF KAZAMACE MATA TA.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*KAZAMACE MATATA*
          ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
  By Ganarious.
Page3

√Mutan Kenya godiya dubu,dubu...๐Ÿ˜˜๐Ÿค๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ

√Ku bi novels Dina a ๐Ÿ‘‰๐Ÿผ ganarious.blogspot.com/
              Ko
๐Ÿ‘‰๐Ÿผgroup din Facebook, *Ganarious book series*.
Thank u.

√ *SANARWA!!!*
KAZAMACE MATATA,kirkiraren labari ne har sunaye,da garurukan ke cikin labarin,idan labarin tayi shige da rayuwanki/ka,ne neman afuwa๐Ÿ‘๐Ÿผ....ba don naci zarafin kowa ba.

       **          **          **
   Sai da ya gama cin abincin,sa'anan Alhaji suleiman ya dubeshi yace 'kanwarka tace kana cikin damuwa,ina kuma sa ran a duniyar nan ta fi kowa sanninka....don haka zamu so jin abinda ke damun.

Nan ya kwashe yanda sukayi da inno ya sanar masu.
Ya kara da fadin "banyi gaggawan yin aure ba,sabida bana son nayi da na sani a rayuwar aurena, a gaskiya hankalina bai kwanta da maganar inno ba,tana fadin hakan, na tsinci kaina cikin wani yanayi,sabida ina tunani zata ruguza min rayuwa.

Rai bace khadijah tace 'gaskiya hakan ba zai yiyu ba....duk wacce inno zata nema maka,ina da tabbacin ba ta gari bace...kar ka manta mahaifiyar yarinyarce abokiyarta, anan abokin barayo,barayonne..sannan fa me halin kirki baya taba birge inno!..tunda ko yarinyar ta birgeta har take neman hada ku aure...! Tooh fa abin shinshinawa ne.
gaskiya yaa munir kar ka amince da haka....wannan karon kam,kayi kunnen kurame,kayi idon makahi da wannan zancen sabida rayuwa ce da idan ansami akasi toh fa sai da tamakon Allah.

Alhaji suleima ya nisa yace "gaskiyar khadijat,idan kagan zata danne maka hakkinka toh kayi magana tunda wuri...
Da haka suka tattauna yanda zasu magance zancen inno.

Engr.munir ya dau tsawon sati biyu,watau jumma'a biyu kenan bai je gidansu ba.
Sai a cikin sati na ukku,sa'anan ta tafi bayan sallan jumma'a kamar kullum

Inno na ganinsa ta hau masifa,tana fadin daman ta ji a jikinta bai yi marhaba ds maganarta ba...daga nan ta shiga kwalan munafurci wai ba don itace ta haife shi ba shiyasa yayi mata haka da makamancinsu.
  Suna tsaka da haka malam Abdullahi ya shigo....ya tarar da tana kwala,cikin rudewa yake tambayarta me ke faruwa.

Wannan dan๐Ÿ‘‰๐Ÿผ...ta nuna munir da yatsa. Sabida ba nice na haife shi ba shi yasa ba zai bi umurni da maganata ba..
...malam Abdullahi cikin matssuwa yace fada min abinda yayi maki na hukuntashi yanzun nan.

Ta share hawaye tace "maganar yarinyar nan ne da na sama masa,tun ranar da na tunkare shi da maganar ya dauke kafa daga gidan nan watau baya so kenan.

Ahaaf...nan da nan malam Abdullahi yashiga balbalin masifa,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba....aure kam kamar anyi an gama,sai dai idan yarinyar ce tace bata son ka.

Ya gama zage munir tas, sa'anan ya fice abinsa.
munir ya bi bayansa,ya je ya bashi hakuri...da kyar ya hakura sannan ya umurci munir da ya tafi ya baiwa inno hakuri.
Ya nufi cikin gida cikin sanyin jiki,ya tarar inno na sa'insa da Habiba akan zancen sa da suwaiba.
Habiba na ganinsa tayi shiru.
Guri ya samu gefen inno ya tsuguna yana me bata hakuri.
Ta ji dadin haka sosai...don haka tace masa ta hakura,kuma tana son zuwa yamma ya zo isa ya yi masa rakiya zuwa gidan su suwaiban don su ga'na da ita.
Ya amsa mata da "toh inni"...sannan yayi godiya ya mike.

Gaskiya inno kin shiga hakkin yaaa munir...fadin habiba dake zaune a gurin tana jifan inno da harara.
Inno ta harareta ba tare da tace mata wani abu ba.
Tunda munir ya koma gida yarasa me keyimasa dadi,ya kasa samun nastuwa sai kai da komowa yake yi tsakanin dakunan gidansa.
Dalilinsa na zuwa gudansu inno shine din ya bata hakuri akan ta hakura da zancen aurensa da suwaiba,..sai kuma ya tarar da makircinta.

Wayar Alhaji suleiman ne ya shigo,ya amsa wayar jiki a mace.
da jin muryansa alhaji suleiman yasan ba'ayi nasara ba, don daman tare suka yanke shawaran da yaje ya sami inno yace ta hakura.

Ya ya kayi da innon,muna jiran kiran ka tun dazun baka kira ba..shiyasa na kiraka yanzun don khadijat ta matsu...fadin alhaji suleiman.

Engr. Munir ya nisa sa'anan ya fadawa alhaji suleiman duk abin da suka faru tsakaninsa da innon.
Hakuri ya bashi,tare da bashi shawaran da ya da'ge da addu'a,Allah shi kawo mafita.

Bayan sallahn magrib munir yayi wanka,ya sanya kananan kaya tare da feshe jikinsa da turaruka masu kamshin gasket,don daman shi ma'abocin son kamshi ne.
Gidan su inno ya nufa...da sallaman sa ya shiga cikin gidan,ya tsakar gidan ya gansu zazzaune suna shan iska...yayi gaisuwa sannan yace wa inno yana son zai je gidan su suwaiba.

HAkura waje sabida jin dadin abinda ya fada....
"TOh toh toh madallah,haka yana da kyau.
TA dubi inda isa ke zaune tace masa "tashi ka raka shi bayan kassuwa".
Ido waje yace 'bayan kassuwa kuma,wane gida zamu na hala!.

Gidan inna ige zaka na raka shi,daga nan za'a nuna maku gidan su suwaiban.
Kin tashi yayi sai da ta dunkula masa zagi sannan ya mike yana tura baki.
har cikin gidan su inna igen engr. Munir ya shiga,ya gaishe su tare da yi masu kyautan kudi masu yawa..
Inna ige ta hada su da jikanta don ya nuna masu gidan su suwaiban.
Ashe ma makwabta ne,gida dayane a tsakaninsu,ganin haka yasa engr.munir ya koma cikin motansa ya gyara parking dai dai gidansu suwaiba...
Jikan inna ige ya shiga cikin gidan don yi masu sallama da suwaiban.

SUn kai kimamin minti arba'in bata fito.
RAnsa ya baci,a ransa kuwa yana fadin za'a fara haka tun yanzun?!!
tsuki yayi...watakila ma wanka ta ke yi,watakila irin matannan ne da basu tsabtace jikin su sai idan za a fita ko idan samarinsu sun zo gun su..haka yake ta sake sake a ransa..
YA sake tsuki yana me duban agogon hannunsa.
ISA ya juyo ya dubeshi yace 'yaa munir da ka fita harkan yarinyar nan mukoma gida ka fadawa inno ba mutuniyar kirki bace,ji fa yanda ta shanya mu anan.
Yana rufe baki suka hango wata na fito wa daga gidan....
Ganin ta nufo su ya basu tabbacin ita ce suwaiban.
Daga isan har engr munir suwaiba suke kallo.
daga yanayin tafiyarta ya raya ransa wannan ba natsattsa bace...tafiyarta kamar zata tashi sama.
Gefen isa ta zo tare da kwan kwasa gilashin.
Engr.munir ya sauke gilashin a hankali yana me dubanta.
Barkan ku da zuwa ta fada.
...wata zuciyar tace ka I...!wannan akwai zakin murya....barkanki kema,engr.ya maida mata.
Maganarta ta yan'sakkwatawa๐Ÿ˜„..tace wane nah ah muneeru ku?.
Isa ya nuna munir da yatsa..bata bata lokaci ba ta zagayo ta gefensa.
Dukowa tayi dai dai windon sa.
SUbhanalillah..!!!.numfashinsake barazanar daukewa,sabida wata irin do'yi da warin hayaki dake tashi daga jikin nata..
Sai ji yayi tana fadin "shii na ka tahi cikin duhu..bara na koma na amso tocilan inna.
Ta juya zata tafi yayi kiranta domin kuwa ya fahimci abinda take nufi.

Yasa hannun sa ya kuna fitilan cikin mota,haske ya bayyana,ya juyo ya dube ta....nan ta'ke zuciyarsa ta shiga raya masa ababe masu yawa.
Itama ido ta sa masa tana me kallonsa...sun kai minti uku a haka sannan tace masa "toh na ganka yanzun.

YA Numfasa domin a takure yake,a matse yake da ya bar gurin.
.....gashi na zo ne da niyar  mu fahimci juna amman kuma baki fito da wuri ba har lokaci ya wuce,dare yayi,sai dai wani lokaci idan na sake zuwa ko?.
Ohoooo...walle wata abikiyata naka sawa man famin,shinassa ban fito da wuri ba.

YAYI ajiyar zuciya yace' toh shikenan,mu zamu koma gida,sai na sake zuwa.
Tayima sa sai da safe..ta juya zata tafi yayi kiranta.
hannu ya sa a aljuhun wandonsa ya ciro kudi batare da ya kirga ba ya mika mata yace gashi a sayi turare ko!!

cikin murna tace a sayi turaren mi!..mi akai da turare abin banza!..tabdi ai wannan kudin ababe da dama za'ayi da su.
Mamakinta yake,sai kallonta yake..shi fa ya bata kudin ne sabida riga kafi....kar ya sake zuwa,ta fito masa da wannan do'yin.
GODIYar ta ya farkar dashi,ba tareda ya amsa ba tayi cikin gida da saurinta.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.