Pages

Wednesday 31 January 2018

Page 33 of SOYAYYARMU

SOYAYYARMU 👫
     By Ganarious
Page3⃣3⃣

Gaisuwa ta mussaman ga mutan KENYA,(NAIROBI)..ALLAH shi bar kauna.

Fatan alkhairi ga makaranta..👍🏼💖

A koda yaushe sabbin updates na nan a 👉🏼 ganarious.blogspot.com/

     **      **        **
Mamee ta juya ta dubi ilham,cikin natsuwa da kwantar da murya tace "ba wai na fadamaki labarin zamana da mahaifinki da danginsa bane don ki tsane su, ko dun ki rama min abinda sukayi min..ah'ah
Bani son  na karajin wai kince zaki rama abinda sukayi min ko makamancin haka...sa'anan kar ki manta laifin wani baya shafin wani,..shi Hisham miye nasa a ciki?
Shiru ilham tayi,ta risunar da kanta kasa.
Mamee ta cigaba da fadin,baki gaji wulakanci ba,don haka rashi daukan wayar sa kamar kina wulakantashi ne don haka ki daina, kinji ko?.
Ta da'ga kai tare da fadin naji mamee..
Nan mamee ta mike tayiwa su Hisham da abokan sa sallama ta shige dakinta.

Shiru shiru ba wanda yayi magana tun tashin mamee.
Hisham ya cije,ya tattaro karfi😆,ya natsar da zuciyarsa zai yi magana.
Yana gyaran murya tare da bude baki,ilham ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu...kamar daman jiran sa take.

Ta kara murtuke fuskanan tata😠...tace "yau ya zamar maka farko,da kuma karshe da zaka fadawa mamata wani abu game dani...bani son alaka da kai ko dole ne😡,na fada maka na fasa auren,don haka ka fita hanyata.😏
Tana kaiwa nan ta mike zata tafi,sai kuma tayo ribas ta dawo baya.
Mind u zan fada maka in advance,ku kasance cikin shiri,kamar yanda na fada maka ina nan akan bakata...sa'anan daya daga cikin family nan zai je kurkutu(prison),nan da sati biyu,bayan ya tafi wani zai bi bayansa,wanda shi idan yaje,ya tafi kenan nan zaiyi sauran rayuwarsa...don haka kana iya fada masu,su kasan ce cikin shiri..who knows watakila ma kana daya daga cikinsu🤔
Nan ta barsu zaune,tayi tafiyarta.
Cikin jin takaici da haushin abin da tayi masa a gaban abokansa,ya mike tsaye rai bacce yace "ku tashi mu tafi,wannan ma katoton wulakanci ne.😏...Mikewa suka yi jiki a sanyaye suka tafi,a hanyarsu ta koma wa kuma ba me magana,tsit kake ji a motan sai dai jefi jefi kaji tsukin Hisham., gashi idanunsa sunyi jajir.
Kamar kullum yau ma Hisham bai rintsa ba,cike yake da haushin abinda  ilham tayi masa a gaban abokansa!...abinda ya fi damuwar kuwa shine furucinta na karshe..
Tashi yayi ya zauna, a ransa yana fadin dole na nemi mafita kafin nan da sati biyu.

      **        **            **
A yayinda dakin ya dauki sanyi,kamshin dadi me sanya ni'ima da nishadi ke tashi.
Lallausar kafet ne shimfide a kasar dakin,wanda kana takawa kafarka na shige wa ciki...daga gefe teburi ne aka zagaya ka kujerun alfarma don zaman baki.
Daga can gefen kuma,teburi gilashi ne da kujerar taya a bayansa.
    *ALHAJI MUSTAPHA B.* shine sunar da ke ke're a wata doguwar kwalba wanda aka dagwarashi saman teburin.
Teburin na dauke da ababe kamar su laptop,takardu dasu files,sai daga gefe aka ajiye wata karamar frame  me kyan gaske dauke da hotonsa da uwar gidan sa Hajiya zubaidah.
A hankali aka budo kofan tare da sallama .
Ya amsa sallama yana me fara'a ganin me shigowan.
Alhaji Abdulmuminu ne,mahaifin hajiya zubaidah...ya shigo ya zauna a daya daga cikin wadannan kujerun.
Alhaji mustapha b.  Wanda jama'a ke kira da Alhaji Buba, ya karaso gun Alhaji Abdulmuminu suka gaisa.
Ya mike ya nufi inda firij ya ke a ajiye ya dauko masa ruwa roba.
Ya sha ya ajiye roban ruwan sannan suka fara tattaunawa akan abinda ya kawo sa.
Alhaji abdulmuminu yayi gyaran murya yace "watau batun kanfanin nan ne na kasar jafan da ake son saidawa.
Alhaji Buba ya daga masa kai,tare da fadin na'am ina jinka alhaji.
Munyi mitin da sauran wadanda muke son hada kai da kudi don sayan wannan kanfanin.....muna sa ran zuwa jibi takardun kanfanin zai iso hannunmu daga can kasar,kuma a ranar ina da mitin a kasar kuwait,don haka nake son ka wakilce  ni,domin kuwa a hannuna takardun  zasu fado,tunda bani nan a ranar sai su fado a hannunka din.
Idan sun iso za ayi mitin a abuja,inda kowa zai zo ganin takardan da idonsa.
nan dai alhaji buba da surikansa alhaji Abdul mumin suka tattauna,daga baya yayimasa sallama sa'anan ya tafi.
Tsaye yake a jikin windon falonsa,daga nan yana hangen mai fita da shiga ta gate din gidan.
Hannayensa na saman kugunsa..
Mai gadi ya wangale gate ,motan kaseem ne ya kunno kai cikin gidan..
Ganin su ba sa ya tashi ko motsawa daga jikin windon ba,sai da suka kai kimamin mintin bakwai da shigowa sannan ya tako ya zauna saman kujeran shim.
Cikin yanayin tausayi kareem yace 'ya daiiiiiiiii...ba mafita ne har yanzun? Gashi saura kwana hudu sati biyu ya cika.
Kai ya girgiza masu kawai.
Kaseem ya nisa yace kun ki bin shawarata,da zaku dauki magana ta ne da sai nace mu tafi gurin mamanta mu fada mata abinda Ilham ke shirin yi...yana rufe baki ,wayar Hisham ya shiga ruri,ganin me kiran yasa shi daure fuska kamar yana gurin.
ya kafa wayar a kunnensa tareda gaishe gaishe.
Daga can bangaren baba lamido ne (Lamido karami)
baya gaisuwa yace wa hisham yazo,yana nemansa yanzun.
Ya ajiye wayar tare yin tsuki.
YA tashi ya shiga dakinsa,ya sauya kaya sannan ya fito.
"Ku tashi kuyimin rakiya zuwa gidan baba lamido..
a gidan baba lamido ya tarar da baba yusuf,yana ganinsu gabansa yace ras!...sabida duk lokacin da zai hadu da wadannan mutanen,toh fa ba wata labari me dadi da zasu fada maka.

BAYan sun sake gaisaw Baba lamido ke fadin ya ya zancen ka da ilham?.
Shiru yayi na dan lokaci sannan yace  mamarta ta amince,amman ilham din ta ki amincewa....

ya tabe baki yace "shi yasa nace ka fita harko kinsu...ga hindo nan .
Ni da sauron yan uwana mun gama magana nan da wata uku za'a daura aurenku.
Cikin shakewar murya,ya shiga basu hankuri..da su hakura da batun aurensa da hindo.
Ai kuwa baba yusuf ya shiga balbala masa masifa.
Kai kasa hisham ke rayawa a zuci cewan mutanen nan basu san abinda ke shirin faruwa da su ba.🤔...a sanyaye yace don Allah baba,ku saurareni.
Su kuwa yi shiru suna jinsa.
don Allah ku bar zancen auren nan sabida abinda ke shirin faruwa a familin nan...kuma kokarina ganin abin be faru ba.
Shashasha......kaji shi da zancen banza! Me ke shirin faruwa? Wani zai mutu ne kokuwa?, ko kuwa idan mun hada ku aure zaka kasheta?..baba lamido ke wannan furucin
Nan dai shiga zazzaga masa maifar irin nasu,daga baya suka tunashhe cewan nan da wata uku aure ba fashi.

Rai bace ya koma cikin mota.
Ganin bacin ransa yasa kaseem da kareem basu tanka masa ba.
kaseem ya ja mota suka tafi.
A gidan hisham ko sai tsuki yake, tun suna daurewa har suka kai ga tan bayarsa abinda ya faru.
Kamar zaiyi kuka yace "mutanen basu isashen hankali😏....da sun san abinda ke shirin faruwa da tunanin hadani aure da hindo ba zai zo masu ba.
natsuwa sukayi suna sauraronsa.
wai fa so suke su dani aure da hindo

Ka fada masu ba ra'ayi mana🤷🏻‍♂...kaseem ke fadin haka.
Na fada masu wallahi....so suke suyi min auren dole.
Toh wallahi idan kayi shiru kai kaso,kuma kai zaka cutu...kareem ya tofa nasa shima.
Da haka dai sukayita banbaminsu har lokacin sallah ya gabato,sukayiwa juna su sallama.

Washe garin ranar da takardun kanfani suka iso hannun alhaji Buba,ya sanar wa sauran mutane..sun kuma shaida masa isowar takardan suke jira,don haka ya gaggauta barin office ya nufi gida don sallamar uwargidansa  zashi tafi abuja.
rakiya tayi masa har zuwa wajen gate inda ya ajiye mota,ganin baza shi dauki lokaci ba yasanya shi barin motan a waje.
ya bude motan don ciro takardun ya nunawa matarsa,sai ya gan ba alaman takardun,ya duba bayan seat din motan,ba alamansa ya koma ya bude bot nan ma babu.😲😧...salati ya shigayi tare da daura hannuwan sa bisa kansa🙆🏻‍♂,Kafin ka sani kayansa sun jike sharkaf.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.