Pages

Tuesday 16 January 2018

Page26 of *SOYAYYARMU*

*SOYAYYARMU*👫
     By A'ishah M.Gana
           *(Ganarious)*
Page2⃣6⃣

ZUciyata,ruhina har zuwa gangan jikina sun ki amincewan fillo zaiyi aure,har sai da suka gan yana shirin zuwa daurin aure.
   Kallonsa kawai nakeyi..ya gama shirinsa tsaf,yana sanya links din hannun rigansa ya juyo ya dube ni mukayi ido hudu..ya kai kimamin minti tara yana kallona ba tareda ya kifta idonsa ba,nima din shi nake kallo.
Ya yi taku zuwa bakin gado,inda nake zaune,ya zauna tare da  kama min yannuna yana me kallon yatsun...ya da'go ya dubeni kamar me tunani,yace "kiyi hankuri maman ilham"
Cikin girgiza kai nace shi kenan abinda zaka fa'da?
Abubuwa da yawa nake son fadamaki...sai kuma yayi shiru.
Nan na shiga yi masa kuka,..ya jayoni jikinsa yana me shafan gadon Bayana.
Muna a haka,wayarsa ta fara kara..a hankali ya da'ga wayar ya dubi screen din wayar sai kuma ya mayar ya ajiye tare da kankameni a jikinsa...
Wayar ta sake kara a karo na biyu,ba dubi inda wayar ba  ballantana ya dauka haka wayar yayita kara be dauka ba..

Kwankwasar kofar da mukaji ya sashi mikewa.
Ilham ce tsaye,ya dauke ta yana cillata sama yana mata wasa..a ajiyeta saman gado kenan tace  masa ai Anakiransa a falo don haka ya fita zuwa falon.
..yana fita safiya ta shigo..."mutane na jiran ango yafito su tafi daurin aure,ashe yana nan yana shan zuma"
Ta'be baki nayi nace 'al'amarin fillo yakan dauremin kai,kamar me iska'
Kila baza'a rasa ba fadin safiya...tana rufe baki,ya shigo rike da Mujaheed,sul-sul safiya ya fice.
Ya karaso inda nake yace kin gama ganin kwaliyan..?
Dubansa nayi da dan harara nace"ai daman ba ni kayiwa ba"
Dariya yayi ya rungumeni,yayimin ra'da akune"wannan kwaliyan taki ce ke kadai"..
Ganin yana rungume dani yasa mujaheed nata ihun ya kankame babansa,ya sake ni ya kamoshi suna wasa itama ilham ta shiga,sai na tsinci kaina cikin farin ciki,rabon da na gan haka...
ya ki zuwa gun daurin aure,yan uwasa suka wakilce shi..sai karfe biyar fillo ya fita,shima din don suna ta damunsa da kira ne.

Tun bayan ficewarsa ban sake ganinsa ba har yan biki sun watse.
Abu kamar wasa har kwana shidda ban sa fillo a ido ba,idan kuma na kira wayarsa ba'a dauka.
Hankalina ya fara tashi,don haka na sanar da safiya,ta bani hankuri takuma bani shawaran da na shiga cikin gida gun yan'uwansa ko mamarsa,ba za su rasa labarin sa ba...haka kuwa nayi,sashen goggoji na nufa tayi farin cikin ganina tana me tanbayata ko nayi mata yaji ne don rabon da ta ganni tun biki na saura sati daya.
Nima cikin farin ciki nace  goggoji nayi haka ne sabida yan rugga sun daina sona ,na rasa laifin me nayi masu.
"Bakiyi masu komaiba"tace dani.
Zaune nake na rasa ta inda zan fara tambayarka ko ta gan fillo...can dabara ta fadomin nace "amarya ta kawo maki gaisuwa kuwa?"
Eh...ai basu jima da barin nan din ba.
Gaba na  naji yayi ras!
Shiru nayi na dan lokaci,sannan nace "sun kyauta.
Daga nan sashen binta na nufa....ko zama banyi ba nace "wai inane sashen amaryanku?
Kamar ya ya fa? Ta tambayeni cikin mamaki
abinda na fada farko shi na sake mai-maita mata.
"Kina nufin  kice bakisan ba'a estate gidan ta yake ba.
A'a wallahi,ban san komai game da ita ba,..a ina gidan ta yake tau?
Na manta da sunar anguwan, cewan binta.

Jiki a mace na koma sashe na ina me tunane-tunane.
Abu kamar wasa,muna batun wata,ba fillo ba alamun fillo,na shiga rudani,na kasa samun sukuni..na rasa wa zan fadawa naji sanyi..safiya ce ta fado min a rai,don haka na dauki wayata na kirata.bugu daya ta dauka...tana fadin hello! Na fashe da kuka.
Ta shiga lallashi tana fadin ki kwantar da hankalinki ki fadamin abinda ke faruwa...
Na dan tsagaita kukan na sanar da ita.
Tayi shiru na dan lokaci,daga baya tace"Gaskiya wannan maganar ya kamata a kaishi gun iyaye.!
Da sauri na girguza kai kamar tana gurin,nace  a a .....kiyayya zai shiga tsakani su.
...tauuu kuma sai a kyaleshi ya na shiga hakinki?ai wannan cin amanace...gaskiya ba zai yiyu ba.
Don Allah safiya kar ki fadawa kowa,pls and pls ina rokonki.
Hmmm...gaskiya banyi alkawari ba,idan dai har maganar ta hanani sukuni,touh fa zan shigo kaduna gobe.
Da haka na dinga bata hankuri,mukayi sallama.

Washe gari na shirya yara na kwashe su zuwa sashen goggoji..kafin mu karasa cikin gidan ta na hangi wata katuwar mota,anyi parking a kofar gidan da ganin wannan motan kasan masu shi sun jiku da kudi..
Ina sallama yara suka shiga ciki da gudu,domin hayewa cinyar goggoji,daman haka sukeyi idan dai mun zo nan.
..ras! Kirjina yayi,ganun mutanen da ke zaune a falon.
Fillo da amaryasa hajiya zubaida..nayi sallama na karasa cikin falon na zauna,mujaheed ya sakko ya nufi gun babansa ya kankameshi...shi kuma ya dauke shi yana masa wasa yana satan kallona.
Daga shi har haj.zubaidan basuyi min magana ba nima ban masu ba.
Kokari nake,ina me dannne zuciyata ka da su  fahimci wani daga gareni,sai dai fillo ya samin ido...tun yana satan kallona har ya kai ga tsaida idonsa gareni,duk na tsargu hakan ya sa na mike na shige bedroom din goggoji.
Da shiga ta fillo yayi sallama ya shigo,ya yi tsaye yana kallona nima kuwa shi nake kallo.muna haka hajiya Zubaida tayi sallama itama ta shigo.ta sami guri ta zauna sa'anan ta dubi fillo tace masa"my one ka ba mu guri zamuyi magana"
Da kamar ba zai fita ba,sai kuma ya fice.
ta dube ni tayi murmushi me dauke da sako..tace"da fatan kina lafiya?
Kallonta kawai nakeyi.
Ta tabe baki tace anyway ba ma sai kin amsa ba..kawai so nake na sanar da ke cewan fa yanzun fillo nawa ne...ni kadai nikadai ke dashi.
Idan har kina son kanki da arziki,kiyi ga'ba abinki,ki yanke duk wani abu da zai hada ku..da fatan zaki fahimce ni?
Tana kaiwa nan ta mike ta fice daga dakin....tana isa falo sukayi sallama da goggoji .
   
    Maganar hajiya Zubaida ya wo yakai a kaina..da zarar na zauna sai kawai ya fadomin.
Yau ma safiyace na kira,na sanar da ita maganar hajiya Zubaida,wannan karon hankuri ta bani tace "...ai na fada maki, kingan maganata ta fara fitowa ko? Suna iyayin komai akan abinda suke so,don haka sai kin hada da addu'o'i,ki tashi tasye da ibada...yanzun haka ba yinsa bane.
kai safiya...ya na sane,da saninsa yake min haka...
Ki kara hakuri,inn shaa Allahu zan samu lokaci na shigo kaduna mu tattauna.

Tunda cikina ya shiga wata bakwai nake ciwon mara,kullum cikin ciwo nake..yau lafiya gobe ba lafiya,sai nake ji kamar zan haihu....gashi na rame,na lallace,kammanina ya canza.
Binta ce kawai ta san halinda nake ciki,cikin ya  uwan fillo don haka kullum tana gurina,ga tausayi.

Zaune nake ina ta tunane,yara kuma suna wasar su sai jinayi anyi sallama..fillo ne ya shigo.mujaheed ya nufe shi ya dauke shi,zai ajiye shi ya kama kuka wai baza shi sauka ba,sai ya nufi cikin daki dashi ba tare da yayimin magana ba hakan yasa ni mikewa na bi bayansa.
Gun wardrob dinsa yake tsaye,da alama yana nema abu ne.na zauna  saman gadon har ya gama abinda yake.
..muna hada ido na dauke kai..shima ya dauke kai yayi hanyar fita.
Da sauri nace"inason zamuyi wata magana da kai fa.
tsak ya tsaya sa'anan ya dawo baya.
Gyaran murya nayi nace..ni fa cikin duhu nake!..shin a wani matsayi nake ne?,yau don Allah bani aron lokacinka ka fitar dani daga wannan duhun..watakila zan fahimce ka.
Kallona yake,bashi da niyar yin magana...haka ya bani damar ci gabawa da magana.
Don Allah yau ka fadamani laifin da nayi maka ni da yarana,ka guje mu baka damu halinda nake ciki ba balantana abinda ke ciki na.
Baka damu da ci da shan mu ba,balle hakina..baka  tunanin wannan yayi kama da cin amana?
Har zuwa lokacin shirun dai yayi bai amsani ba.
Nan kuka ya zomin..ina fadin ka amsa ni mana! Me nayi maka haka!,yau watan ka daya da sati biyu kenan rabon da ka tako wannan gidan,ko baka zo don ni ba ka zo don yaranka..
Sai da kukan ya tsananta sa'anan yayi gyaran murya yace "bakiyi min komai ba.
Abubuwa ne sukayimin yawa,ina kuma zirga zirgan gyaran gidana,da man nufi na idan komai yayi saiti sai na zo na kwashe ku mukoma can din,sabida kar ki gan kamar an shiga hakinki.

na tsai da kukan nace "ka sami gida fa kace?
gira ya da'ga sannan yace eh..
cikin bacin rai nace wannan kuma fa ,ba gida bane??
Wannan giidanki ne,wancan din kuma gida na ne.!as far as kina matata kuma kina son ganin ko zama dani,toh fa zaki tattara naki da yara ku dawo gidana.
A fusace na da'ga masa hannun tare da fadin kaiii...macuci!ni kake fadawa haka??mahaifina zakayiwa butulci? Toh wallahi baka isa ba!.
Idona ya rufe sabida bacin rai asalima ban taba bacin rai irinta ranar ba, na shiga zaginsa...
ya mike zai fita,gefe na kuwa kayan wasan mujaheed ne,na dauke su ina ta jifan sa da shi har ya fice.

KUKA nakeyi sosai raina ya baci,tunda nake da fillo ban taba jin na tsane shi ba sai a ranar duk da abinda yaKe min bana jin haushinsa.
Sai nake ganin baiyi wa babana adalci ba.
Ina kuka ina shirya kayana da na yara,na hada muka nufi gida.

Mamata ta rude ganin ina kuka,ta shiga tambayata abina ya faru,amman kuka bai barni nayi mata bayani ba, don haka ta fita harkata har sai da nayi me isata nayi shiru.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.