Pages

Friday 21 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫.
   By Ganarious(Al-Ansar writters member)
3⃣
    My baby namesake na shiga hakkinki dayawa,sabida son zuciya..idona ya rufe sabida na kasa manta abinda babanki yayimin har ina neman cutar dake, i am very very sorry ta karasa maganar tana kwala.
 Da sauri nace please mamee dnt do this to me wallahi bakiyi min komai ba nice na sa'ba maki kuma inn shaa Allah bazan sake ba.
A a ilham bakiyimin komai ba,idan ma baki yafemin min ba hakkinki zai kama ni....kalli fa yanda kika rame ?.. Kema kinsan ba abinda nafi kaunar gani a duniyar nan kamar naganki dubul-dubul dake,son zuciya bai barni na gan wannan raman ba.... Kiyi hankuri ki kwantar da hankalinki ko jikin zai dawo kin my girl,..kai kawai na daga mata.
Idan ma auren hisham ne zai kawo maki kwanciyar hankali,toh na amince har cikin zuciyarta ki aureshi....tana kaiwa nan ta mike,har ta kai kofar fita ta juyo tace min ki fito parlo abokan hisham na nan.
Bayan fitar ta na koma gaban madubi na kurawa jikina ido,a gaskiya rame sosai,na kuma dade da sanin na rame shi yasa idan zanje gaida mamee nake sanya hijabi sabida tun ina karama tana jindadi idan ta gan jikina yayu bul bul..
Humura kawai na shafa sa'anan na sanya bra,tare da zura jallabiyata na fito falo.Farin cikinsu ya bayyana don ganina.bayan gaisawa kaseem yace subhanallahi...a gaskiya ilham kina cikin wani yanayi..
Murmushi kawai nayi batare da na tanka shi ba..kareem yace kamar yanda abokinmu ke ciki bahhh.gaskiya wannan soyayyar a jini yake.mun dan jima suna zolayyata daga bisani kaseem     yace wannan punishment yayi wa Hisham tsauri don Allah a tausaya ya sassauta mashi pls ilham.
Ayyah ni da Hisham kuma sai...
Sai mutuwa ka raba ku,kareem ne ya tareni da wannan zancen ba tare da na kai ba
Hmmm..
Mikewa kareem yayi yace zamu tafi,Don Allah ki biyo mu ku gaisa da shi.
Kai kawai na daga masu alamar baza ni je ba.
Sunyi juyin duniyar nan wai na tashi na bisu,ni ma kuma nayi kememe,sai da suka gan alamar bani niyar tashi sa'anan sukayimin sallama.har sun kai bakin kofa sai ga mamee ta fito tace masu tafiyan kenan ???
Lokaci guda suka juyo tare da sunkuyar da kai.
Eh...zamu tafi rakiya.
Ok...idan ya dawo tafiya kuce mashi ina nemansa.
Inn shaa Allah zamu fadamashi.
 Bayan fitansu mamee ta dawo kusa dani ta zauna,"Baby namesake Allah soyayyar ta zama aure...
Mamee..?? Wace soyayyar ?
Soyayyarki da Hisham mana.
Cikin mamaki nake kallonta..Ai ni na fasa.
Sabida me kika fasa ?
Nidai kawai na fasa
Sai kin fadi dalilin ki
A a...gaskiya mamee baki son na aure shi kina dai pretending ne,ni kuma abinda bakiso bana fatan nayi shi.
Murmushi mamee tayi sa'anan ta dawo kusa dani ta kamo hannuwana tana murza yan yatsuna...A'isha.tayi kirana,na dago na kalleta.
Kin yarda dani ?
Eh ...sosai mamee
Toh har ga Allah wannan auren ina marhaba dashi,da farko dai ban amince ba amman a yanzun abin yanayimun dadi,kin ko san wannan soyayyar na ku tun kina ciki ?  Yes tun kina ciki Hisham ke sonki.
Kicin zaro ido nace"Hisham fa kikace ?
Tabbas Hisham,tun kina ciki yake sonki..don haka wannan al'amarin sai Allah
Mamee daman kinsan Hisham ne sosai haka ?
Batare da ta amsa ba ta mike tace idan ya dawo nayi maki alkawari zan sanar daku komai da komai akan rayuwata da dangin babanki.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.