Pages

Saturday 14 December 2019

RIKICHI2

RIKICHI 2
  By Ganarious

  Duk ranar Asabar aiki muke a gidan mu kamar baza'a yi ba kuma.
Sakamakon irin baccin da nake ji, na haye kan gado bayan da na idar da sallar Asubahi.
Kamar minti talatin da kwanciyata naji saukan hannun a jikina ana bugu na, a firgice na mike, duk da na riga da nasan ko wacece.
.....tashi don ubanki, yau duk aikin gidan nan kece zakiyi su.
A sanyaye na sauko kan gado zan nufi hanyar toilet.
Ta fizgo..hade da fadin shegen wankan nan da zai dauke ki awa da awanin baza kiyi shi ba sai kin gama min aiki. ... Wuce kije ki gama komai har breakfast, kamin yara su tashi.
Cikin rashin damuwa na karasa gun wardrob domin sauya kayan bacci, zuwa ta aikin gida. lokuta da dama idan dai abba yayi sakamakon fita, ire iren abubuwan da ke faruwa kenan, idan da sabo na saba.
Tunda na fito daga dakina har na kai kicin ban hadu da kowa ba hatta masu aiki duk suna daki.
Sai da na kammala komai, sa'anan Rahama da Hauwa suka fito, ko waccensu da dar-dar takeyi. Na wuce ta tsakiyansu ba tare da na tamkamasu ba.
Dakin yara na nufa, na hada masu ruwan zafi nayi masu wanka tare da sanya masu kayan islamiya sannan muka fito na hada masu abin kari.
Suna tsaka da ci, anty ta fito.
"Sannu da aiki zee"
Yauwa anty kin tashi?
Eh! Kin gama aikin ne?

Eh, na gama, na bata amsa.
Yauwa ko ke fa! Idan banyi maki haka ba baza ki iya komai ba wai ke yar gata.

Mmmh... Wallahi Anty ke ce dai kike ganin ban iya komai ba.
 Shikenan, a hado min nawa abin karin.
Na nufi kitchen na hado mata. Thanks ta fada hade da murmushi.
Je ki dakina ki tado Amira ta yi kari, amman kiyi mata brush tukun kamin ku fito, kinsan ta da rigimar ta!
Na mike zan tafi dakin ta, sai kuma tace masu aiki fa, kin kai masu abin karin su kuwa?
A'a, idan su Layu sun gama zasu mika masu.

No! Ke ce zaki kai masu, ta fada ba tare da ta dube ni ba.
Kai...Anty!
Eh... Har su Rahama ma kece zaki kai masu, training nake baki idan kinyi aure gidan yawa shikenan kin huta.

Bayan kowa yayi break, anyi wanka, anty ta kwashi yara don ta sauke su a islamiya, ita kuma ta wuce gun kitso daga nan.
Suna wuce wa na fada bayi, nayi wanka.
Rahama! Rahama!!
Na'am Anty zee gani.
 Don Allah ku daura abincin rana da wuri,ni zan kwanta kuma kar wace ta tashe ni
Tana wucewa na haye saman gado sai bacci.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.