Pages

Wednesday 18 December 2019

RIKICHI 3

      RIKICHI episode 3
Assalamu Alaikum Ganarious Blog viewers🙋! I appreciates you all.

if really my stories are interesting, please drop your comments.
You can also email me at ganarious98@gmail.com

       *****************
Cikin barci ana kwankwaso min kofa. A hankali na bude idanuwa na, hade da yin yar siririyar tsaki a yayinda nake saukowa daga saman gadon.
"bana fada maku idan ina barci a daina tashina ba? Na fada a yayinda na bude kofar.
   Anty ce tace a ta'da ke, dazun ta aiko kofar a rufe sai tace a kyaleki, Abba ma ya dawo yayi tambayarki mun fada masa kina barci, shine yace idan kin tashi ace maki ki kira shi a waya ku gaisa. Yanzun kuma kinyi bakuwa, shine Anty tace na tado ki, kiyi sallah.
Tunda ta faro maganar bata tsaya ba, sai da ta kai karshe, ni kuwa na tsira mata ido.
Yanzun bakuwar ta zo?
Tun dazun fa ta zo, don har tayi sallah a dakin Anty.
   Ina take yanzun?
Tana falon Anty.
Ok, je ki gani nan zuwa!
   Daman da nayi wanka ban sanya komai a jikina ba, bada dogon rigan da na zira kawai, don haka na sanya kaya hade da undies sa'anan na fito zuwa falon Anty.

   Da sallamata na shiga, ganin ko wacece yasa na dan murmusa hade da fadin "Ayyah, ashe ke ce kika zo, sannu da zuwa"
Itama cikin Anashuwa ta amsa "eh ni ce, ina yini"
Lafiya lau, ya gida?
Lafiya lau suke, ta maida min martani, nan dai muka yi yan gaishe gaishe, bayan nan sai kuma mukayi shiru dukan mu.
 Mun dan dauki lokaci, ba wace ta kara cewa ufan, bayan gaisuwart, daga bisani  nace mata tou ya ya zancen maganar?
  Eh daman shi ya kawo ni.
Okey, tashi muje daki na, sabida kar yaran nan su zo suna damun mu.
Har ta mike nace "oh! Dan bani minti shida nayi sallah"
Murmushi tayi tare da fadin babu damuwa, na umurci layu ta kwaso mata hoto albums din mu.

Bayan na idar da sallah muka shige dakina wanda yake tashin kamshi ta alfarma! Gashi sanyi A.C ya garwaye dakin.
Tou bisimillah, ke nake sauraro, ha fadi hakan A yayin da nake gyara zamana.
  Da farko dai sunana maryam Idris isah, nayi karatun primary da secondary a El-Amin da ke garin Minna. Mahaifina Alhaji idris haifafen garin Suleja ne, mahaifita kuwa yar garin kontagora ce sunarta Amina, mu kuma muna kiran ta da Umma.
 
        **************
TUNA BAYA(asalin labari)
         **************
Mahaifin Alhaji Idris a lokacin shine Sarkin Noma, yana da dan arziki dai dai gwargwado. Matansa biyu, da hajiya Asabe da Hajiya Larai.
Hajiya Asabe itace babba, ya'yanta goma sha Uku, maza biyu, mata goma sha daya.
Sai hajiya Larai, mahaifiyar Alhaji idris kenan, me ya'ya bakwai. Uku maza hudu mata.
Alhaji idris na da kimamin shekaru goma sha biyu zuwa uku, mahaifin su ya sanya su a primary, ba'a shekare ba mahaifin nasu ya soma ciwo. A wannan shekaran basu samu natsuwar yin gona ba, gashi sun sayar da anfanin gonar su don nemawa mahaifinsu magani.
Sun je asibitoci ba iyaka, amma an kasa gano ciwon, daga karshe likitoci sun basu shawara da su koma gargajiya.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.