Pages

Sunday 23 July 2017

SOYAYYAR MU👫

SOYAYYAR MU👫
       By Ganarious
7⃣
Bazan iyacewa ga adadin mintuna ko awanni da nayi a wannan yanayin ba...maganar da naji ne yasa ni bude ido shima dishi-dishi watau blur-blur nake ta gani.
Me maganar ya karaso inda nake yana fadin "mutunshee"...."mutunshe kuwa?
A hankali na fara gani..wani kyakyawan matashi bafillace ne ya tsuguno dadai fuskata yana tambayar "mutumshee "
Na murza ido tare da yin salati,ina fadin ina yan uwana...domin kuwa gari ya fara duhu.
    Ya juya yana waige waige..'yo ai ke dai ce a wannan dajin.
Cikin razana nace a a...bani kadai bace muna da yawa,mun zo fitsari ne anan.
'yo tau sun tafi sun barki kina barshi.
Yana fadin haka na fashe da kuka ,nace mashi ya rakani wajan daji inda aka ajiye motoci ko suna nan.
Na fadamaki ba kowa a wannan dajin sai ke dai..sai kuma ni da shanaye na....kuka na shiga yi sosai shi kuwa dan filloba abinda yake sai kallo na.sai da kaina ya fara sara sa'anan na saurara kukan nace mashi 'ko zaka iya taimakamin ka rakani cikin yola ko zan hadu da sauran yan uwana..'kai ya girgiza tareda fadin daga gun kiwo nake.yau watanni na biyar da barin gida.
Da sauri na durkusa ina rokonsa "Don Allah kataimakeni ka nunamin hanyar da zaikaini garin yola.
"kalli nan"yayi nunin gefen dama da dan yatsa,idan kika shiga cikin wannan dajin sai kiyita mikewa har sai kinkai inda ruwa yake sai kibi hannun damanki ki mike zakishiga yola.
   Da sauri na zaro ido shiko yana kaiwa nan ya mike abinsa..nima na mike nace mashi awa nawa ne zai kaini yolan?
 Awa?....miye haka kuma?
Ina nufin zan iyakaiwa cikin kalilan lokaci?
'yo ai ni bansan yaya saurinki yake ba,amman idan kina da sauri xaki iya kaiwa cikin na kwana uku.....yanzun don Allah bazaka sada ni da garin yola ba?
 Yo kebaki da fahimta ne?..na fadamaki daga kiwo na dawo,koma idan nace zan rakaki yaya zanyi da shanayen zan barsu anan din ne?.ya fadin haka ya fara kora shanayensa ina kallon sunyi nisa da ni gashi na kasa samun mafita komai ya daburcemin,lissafi da tunani duk sun tsaya tsaf.
  Cikin sauri na bishi inakiran dan fillo...bai tsayabba har sai da na kai inda yake nace yanzun don Allah kana iya wucewa kabarni a wannan dajin ba tare da ka taimakamin ba?
"yo ai ni bansan mutumshee ki aljan bashee..kuma ai na fada maki dalilinda yasa bazan taimaka maki ba.
Toh naji yanzun na bika gida,idan ka ajiye shanaye zaka rakani yolan?
Sai da ya jima kamar me tunanin wani abu sa'anan tace toh...ba damuwa.
Muna ta tafiya har duhu ya gabato tsoro ya fara mamayemin zuciya don tunda nake ban taba kaiwa war wannan lokacin  Waje ba,balle kuma a daji...muna cikin tafiya nace mashi mun kusan kaiwa rugganku kuwa? Yace a a...sai gobe dadaddare idan kuma shanaye sun tsaya cin abinci sai jibi da safe zamu isa.
  Innalillahi'wa'ina'ilaihirrajiun kawai na ke furtawa,zazzafan hawaye ke gangarowa saman kuncina...sunayen Allah kuwa harda wanda bana yawaita kira duk sakira nake ina fadin ya'Allah ka cece ni kai maida ni gida.
Duhu yayi sosai tsoro ya da'da kama ni,karkashi wata bishiya dan fillo ya sami guri ya zauna yace mu huta anan,gobe sai mu cigaba da tafiyar.
'a nan'...nace mashi cikin muryan kuka
Yo ina kike tunani da?...
Ban amsa shi.
Dan fillo yayi nisa da baccinsa ni kuwa a tsaye nake sai aikin kuka....can sai ya farka yace "yo a tsaye zakiyi barshin?...shiyasa nace ke ba mutun shee ba...nan ma ban tanka shi ba.sai  kuka kawai nakeyi..
  A haka ko na kwana tsaye...gari ya fara washewa,haske ya bayyana...dan fillo na farkawa ya ganni tsaye yace yo a tsayen kikayi barshi?..yana maganar ne tare da mikewa ya fiddo goran ruwansa ya kuskure baki tare da wanke fuska sa"anan na tuna ina da water bottle a school bag dake goye a bayana,na sauke jakkata don ciro goran ruwan,na ci karo da wata farar pepan wasika,sai ina mamakin yanda akayi wanan takardar ta zo jakkata.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.