๐๐๐๐
*KAZAMA CE MATA TA*
๐๐๐๐
Written by Ganarious.
Page8
√... Hidayat yusuf, Naziha yareema, rukky d/daji, salamat umar, zuwairah shehu, Ameena aminu bayero,sa'adat Ahmad.......i heart u all.
√... Gaisuwa ta ga marubata,,Allah ubangiji ya kara kai'fin basira.
√... @mss ganarious on instagram.
√... ganarious.blogspot.com/ shine inda za'a sami latest update ko na ce page release,sa'anan akwai posts game da gyaran kai (gashi)da kuma yanda zakiyi/zakayi man kitso da sauran su dai a gida..
<><>√... Ya ke yar' uwa, ki lura mana cewan zaman banza bai yi ba a rayuwa.๐คท๐ป♀
Me Zai hana ki natsu,ki kwantar da hankali ki tambayi kanki 'wace irin baiwa ce Allah ya halittoni da ita?
Idan ki gaza ganowa sai ki natsu kiyi tunanin abinda kika fi iyawa da kuma kware wa,,...kai ko baki iya ba idan har kika nache cewan da izinin Allah zakiyi abu kaza,idan har kika sa kai, toh wabi'iznillah sai kin iya.
Don haka ina me bamu shawarwari da mu tashi tsaye mu nemawa kan mu abinyi,ba sai mun dogara ga aikin gwamnati ba ko ga iyayenmu ba.
Idan kuma kinyi niyar aiwatar ko yin wani abu sai kiyi tunani kigan, shhin abin na tafiya da zamani.
Misali....
Inn'shaa'Allah zani samu lokaci nayi rubutu akan wannan,don kar na cika wannan page din da surutu.
Afwan๐๐ผ
** ** **
Zaunar da ita yayi a saman gadonsa.
Ya karasa gun wardrob dinsa ya fiddo guntun wanda me aljuhu gefe gefensa wanda maza suka fi kira da 3quater.
Singlet ya saka, bayan da ya sanya wando...sa'anan ya ratsa ta gefe-gefe, ya fita zuwa kitchen .
Tsintsiyar shara hade da parker ya dauko,yana shigowa ya shiga tattara gilashi ko nace kwalaben da suka tarwatse a kasa...har izuwa wannan lokacin idon ta a runtse take.
Cikin takaici ya dube ta...."tashi ki fita"
A hankali ta bude idonta tana duban sa,ganin da kaya a jikinsa ya sanya ta bude idanun fully...nan ta mike ta ficce daga dakinsa.
A hankali ya janyo kujera tare da ambata "bismillahi" sannan ya zauna.
Ya sa hannu yajanyo kulan abinci gabansa tareda murda murfin.
Tafiyar tsu-tsa ya soma ji a kirjinsa....a dalilin yin ido da abincin da suwaiba ta girka.
Da sauri ya maida murfin ya rufe.
Hannu yasa ya tallafa fuskar sa....."agaskiya inno ta cuce ni,ta cuce ni......sam suwaiba ba kala ta ba ce.
Lokaci daya yayi tsuki tare da mikewa,dakin sa ya nufa ya sami wata yar jakka ya dawo ya saka kulan aciki sa'anan ya fisgi makulan motan sa.
Sai da yayi tafiya me nisa sa'anan ya hadu da wasu almajirai su uku.
Parkin yayi,ya fito daga cikin mota,....cikin da'ga murya yayi kiran almajiran don sunyi dan nisa da shi, sai da wani ya taimaka masa,yayi kiransu.
A guje suka iso gunsa,ya shiga shafa kansu yana me tambayar sunayensu.
Bayan sun gama bashi amsa ya bude motarsa ya ciro jakar abincin sannan ya amshi robobinsu ya raba masu..
Bayan ya zuba ma kowannensu ya umurce su da su biyo shi...
Wanni shago dake kusa suka shiga, nan ya sayiwa ko wannensu silipas da sabulun wanka da ta wanki.
Ganin farinciki da anashuwa a fuskar sa ya sanya shi tsintan kansa cikin farin ciki, engr. Munir yana matukar son ganin wani yana farin ciki a dalilinsa......
Daga gurin gidan cin abinci, watau restaurant ya nufa, sai da ya cika cikinsa tam, yanda ba zai ji yunwa ba, har washe gari sa'anan ya nufi gidan abokinsa kuma amininsa Sa'ad.
"kai shegen duniya,daga yin aure sai kayi tsadan gani?....sa'ad ne ke wannan magana yana me zolayansa.
....me ya hana kai ka neme ni?
Haba......ai duk wanda akayi wa haka an zalunce shi,ace kuna tsakiya da shan honey moon sai kawai na zo na takura maku?
Tsuki engr. Munir yayi, a yayinda yake kokarin zama.
Dai dai nan matar sa'ad ta fito cikin fara'a.
Marhaba da zuwa ango......ka yi wuyar gani., tana kaiwa nan ta mike ta nufi kitchen.
"toh ya?"
...."mtssww...dai dai
Ban gane dai dai ba, wannan tsukin kuma fa? Anya kana dai dain kuwa.? Ko dai potacot din ne baiyi maka dadi ba?
Nop.....aikin potacot kam,sai dai hamdallah,duk da na ji jiki sosai.
Sorry.....Allah shi taimaka.
Ameen.
Toh yaya Amaryan mu?
Dogon tsuki engr.munir yayi wanda bai da masaniyar lokacin da yayi sa.
Matar sa'ad ce ta fito rike da wanda ke dauke da kayan mar-mari,ya jawo stol ta ajiye a tsakiyansu sannan ta daura tire din a sama.
.....'bisimillah ta fada, a yayinda ta nemi guri kusa da mijin ta ta zauna.
Thanks....ya fada....a yayinda suka soma hira da labarin ababe da suke faruwa a doran kasa.
Sai da magrib ya gabatoh, sannan yayi masu sallama.....
Yaushe za'a kawo mana Amarya ne? Fadin sa'adah matar sa'ad.
Zani kawo maki ita, inn'shaa'Allah.
Toh shikenan,ina jira, amman kafin nan a mika gaisuwata gareta..
Sa'ad yayi masa rakiyah gun motansa.
..."kai ya ne.......na fa karanci damuwa a tare da kai, me ke faruwa ne?
Tsuki ya sake yi, ya cigaba da kokarin bude murfin motansa.
Sa'ad ya rike murfin kofan...."whats going on"
Ya juyo ya dubi sa'ad din cikin lumshe idanu ya shiga fadin....."a gaskiya inno ta cucheni,sam sam suwaiba ba kala ta bace, bata canchanchi da na zauna da ita a matsayin mata ba...wallahi kazama ce, Kazaman ma ta karshe...ko girki fa bata iya ba! Iyayenta sun cuceta ba abinda suka koya mata sai kazanta...
Calm down......calm down, sa'ad ya fada yana me dafe kirjin engr. Munir ganin yanda ransa ya baci,idonsa na batun rufewa.
Ka tafi gida kawai inn"shaa"allah gobe zamu hadu mu tattauna.
A masallacin da ke kusa da gidan sa yayi parking,ya fito zuwa haraban masallacin ya yi alwalansa, sa'anan ya shiga.
Bai fito ba sai da ya tabbatar ya gabatar da sallan isha'i, sannan ya karasa gida.
Ya jima xaune a falon,ganin bai ji motsinta ba,ya tabbatar masa tayi bacci don haka ya rufe gida ya shige dakinsa.
Kashe gari,, sai da ya kammala shirinsa tsaf,sannan ya fito, ya nufi kitchen ya hada shayinsa.
Har ya fito zuwa gun motansa sai kuma wata zuciyar ta raya masa da ya dubo ta, don haka ya juya ya nufi hanyar dakinta.
Yana bude kofan 'wata irin doyi ta bugi hancinsa....da kyar ya kuntsa kai dakin.
Tana ganinsa a rufe fuskarta tare da juyawa gefe...."ina kwana?
Ta'be baki yayi,tuna dalilinta na yin haka.
'me ke wari a dakin nan"
Shiru tayi bata amsa ba.
Anyway nasan daga bayin nan ne,don haka ki shiga ki wanke shi, kin ji ko?
Awo....na jiya ta maida masa.
Ya ja kofan yayi tafiyarsa.
Yau kam aiki yayi masa yawa,sai bayan sallan la'asar ya kammala komai a office din,don haka yayi haraman komawa gida.
Wata zuciyar ta raya masa da ya fara zuwa gidan abinci ya cika cikinsa, a yayinda wata ke gargadinsa tana me fada masa..."me kake tunanin mutane zasu fada akan ka idan sun ganka a gidann cin abinci?...don haka ya dauki shawaran zuciyarsa me gargadinsa
A hanyarsa ta koma wa gida, ya biya wata shago. Indomie da kifin gongoni ya saya sannan ya nufi gida.
Kai tsaye kitchen ya nufa da isar sa gida.....sabida matsanancin yunwan dake tattare da shi har ya sauya kalar idanunsa
Yana shiga kitchen yayi karo da sarauniyarsa,ka da kai tayi,ta ratsa ta gefensa za fita.
Ina zaki tafi?....ya fadi haka a yayinda ya rike mata hannu.
Ba tare da ta dube shi ba tace'zani jira, ka gama da kitchen din.
Sabida me?? Ya fada yana duban ta kasa kasa
Shiru tayi bata amsa ba.
"kar ki manta na fada maki da cewan kar ki sake ki fita a wannan kitchen ba tareda kin tsaftace shi ba,...yanzun da kike shirin fita, shi abincin da kika daura fa? Sakin hannunta yayi..."ko ma ki ci gaba da abinda kikeyi"
Ya na'da hannun rigansa ya kunna dayan gefen gas, a yayinda gimbiyarsa ke girkinta da dayan bangaren.
Tukunya ya dauko ya da ruwa ya wanke,sannan ya zuba ruwa ya daura a saman gas din.
Tana ganin ya fiddo indomien sa a leda tace ..."laaah,ai shinkafa na daura.
Nop....ki ci abinki.
Kai kuma fa?
Gashi kina ganin zani dafa indomie!
Ai kuwa dai banji dadi ba,wwnnan abincin har da kai na sa.
Ya juya ya dube ta sukayi ido hudu,nan ta sake kauda kai.
"daga yau idan zaki daura abinci,kiyi dai dai cikin ki.
Don me?...ta nemi sani.
Sabida bazan iya kallon abincin da kika girka ba,ballantana ma ci.
Don me touhh, girkina da ke uban dadi? Kowa fa na son cin girkina,shi nassa lokacin da nake gida duk ranar da nayi girki sai sashen mu ya cika kowa na farincikin zasu ci me dandano.......
Dubanta yake ido a lumshe kamar me jin bacci,idan ba kasan engr. Munir ba zaka dauka wata sabon salon kallo, ko kuma kayi zaton da gangan ya ke wannan kallon don rudar da mutun.
So da yawa yan mata na shiga rudu a duk lokacin da yayi masu irin wannan kallon,su kasa sukuni suyi zaton a sane yake yinsa.....maza kuwa zolayansa sukeyi suna fadin mu ba yan mata bane da zaka rudar da wannan kallon naka....
Abinda mutane da dama basu fahimta ba shine shi wannan kallon halitta ne da Allah yayi yoshi dashi, idan har zai natsu ya saurari zancen mutum tauh lallai haka zai dunga kallon me magana...
Bayan da ta gama maganarta ya juya ya zuba indominsa a tukunya ba tare da ya ce mata ufan ba.
Ya ciro tattasai da albasa, nan ya shiga yin komai a natse ita kuwa ba abinda takeyi sai binsa da ido.
Duk abinda ya dauko xai yi amfani da, sai ya wanke kafin yayi amfani da,idan kuma ya gama aiki da shi ya wanke ya mayar gun da ya dauko, da haka yayi hada indomin da ko a t.v ba taba ganin irin sa ba.
Ba abinda takeyi sai hadiyan yawu๐
Plate ya dauko ya juye indomin din bayan da ta dahu...bai tsaya wanke tukunyat ba, sabida yunwa da ta addabe shi.
Ya isa gun dnining sai ya tuna ai bai dauko fork ba, don haka ya nufi kitche a hanzarce.
Sawaiba ce tsaye jikin sink tana lasar da tsintar ragowar indomi da suka lake a jikin tukunyat.
Tana ganinsa ta matsa gefe cikin jin kunya.
Tauhhh masu karatu gare ku, idan kai/ke ce engr. Munir yaya zaki/ka yi, ko nace me zaka/ka yi?
Ganarious dinku ce, one love๐
Read More »