Pages

Monday 16 April 2018

Page40, of SOYAYYARMU 👫

SOYAYYAR MU👫
       By Ganarious.
4⃣0⃣

Salaam yan'uwa maza da mata,ina yimana fatan alkhairi..ina me baku hakuri akan rashin chigabawa kwana biyu,kunsan halin rayuwa yau da gobe sai Allah..ina maku godiya sosai da kulawarku,thanks alots😘

√•mutan *KENYA* thanks alot,one love keep us together.💞

√• insightful Nura Abubakar *(elnas)* u mean so much 2 me..even when we can't get  intouch with each other,i wnt u to know that d memory we had would 4ever linger in💖.thanks 4 d courage and support, even when it was 4 a short period.


           **         **       **
  Bata jima da shiga ba, ta fito da shirin ta.
Ganin irin shigar da tayi,ya sanya shi yin murmushi domin kuwa rabon da ya gan tayi irin wannan shigar, tun farkon haduwarsu.

Riga👕 da wando👖 ce  a jikinta.rigar cikin ta sa'ka ta cikin wandon,sa'anan ta da'gora wata rigat me dogon hannu🧥 a saman na cikin,sai dai wannan rigar ta wajan, botins din ta a  bude suke don haka kana ganin rigan cikin.
Tayi pakin gashin kanta👱🏻‍♀,me sulbi da kuma tsawo ta kame shi da ribon a baya, sa'anan ta da'gora face-cap🧢...kafar ta kuwa sneakers 👟ne masu kyan gaske,ga kuma🎒 ta Gucci... idan ba anfadawa me karatu cewan da'ga nigeria ta fito ba,zai dauka bakar baturiya ce.

Tana isowa gabansa,ta kame kugu.!
"I'm set" ta fada a takaice.
ya mike yana me kallon ta da'ga sama zuwa kasa...ya karasa gab da ita,tare da kai bakinsa setin kunenta👂🏼.."kinyi kyau sosai,sai dai wannan shigar, doesn't show ur identity as a muslim..kar ki manta nigeria zamu tafi"
And so what🤷🏻‍♀...ta fada tana me kallonsa.
 "go back inn, and change..ya bata amsa, a yayinda yake kallon hips din ta,domin kuwa wandon ya fito da  surarta,ga ta daman tabarakallah,hips kamar ta  jenifer lopez.
Ganin kallon da yakeyi mata ya sa ta tsarguwa,ta dube shi tare  da yatsine fuska,ta turo baki sa'anan ta juya ta koma ciki.
dariya ya shiya yi,yana me farin cikin cin nasara.

Jim kadan ta fito..banbancin shirin da ta baya kadance,domin kuwa wando ta sauya zuwa skirt,sai kuma hular da ta sauya zuwa mayafi ta laulayi kanta kamar hijabi🧕🏻.
Tana fitowa ya rungume,ya sumbaci goshinta tareda fadin "ko ke fa?"....nan ya rike mata hannu suka fita zuwa airport.

Zaune suke a kujerar da aka tanadar domin masu jiran jirgi.
Hisham ya dube ta yace "me kike tunani yanzun?
Na me fa?.ta tambaya ba tare da ta dube shi ba.

Uhmmm..kin fini sanin abinda nake nufi da haka..."i mean about the story in that letter"
Shiru tayi na dan lokaci,shi kuwa banda kallonta ba abinda yake yi...ganin shirun yayi yawa yasa shi poking🖕🏻 dinta da yatsarsa.
Ta juyo ta dubeshi tare da aJiyar zuci..."i am still thinking".
suna a hakan shiru shiru ba wanda yace da wani kala...ta da'go ta dubeshi "ina son kayi min wata alfarma"..
😳Ido waje yace "huh..
Ta da'ga masa gira,a yayinda take shirin yin magana ya dakatar da ita...hanzari ba gudu ba,kafin ki fadi bukatarki,ni ma da abinda nake son kiyimin idan har kina son nayi maki naki.
Murmushi tayi "da ka saurari abinda zani fa'da tukun".
Nop.....idan kin yarda ni zan fara magana..
Hakan yafi?
Eh ya fada tareda da'ga kafada.
Alright,thats not a problem at all don haka ina sauraronka.
Shiru yayi yana me kallonta kamar me tunanin wani abu.
Ta sa yatsarta ta ja masa hanci tare da fadi"hey i am listing....
No...ki fara fadin naki naji.
Toh idan kuma na fadi abinda baza ka iya ba fa?
Duk abinda zaki fada a shirye nake nayi matukar zakiyi abinda na fada nima.
Tayi murmushi tare da ta'fa hannuwanta...."ok ok, so nake ka kashe hajiya zubaida..kuma yankan rago zaka yi mata.
😳😨what?....ya fada
Yes!😉 ta fada...
Ya shiga girgiza kai....no no,ba abinda ke mind dinki kenan ba.ba kuma shi kikayi niyar furtawa ba.
Kamar ya ya 🤷🏻‍♀...ba ka ganin abinda ke rubuce a wasikar?..har abinda ya fi  yankan rago ma zani so nayi mata.
Murya kasa-kasa...yace tell me this is not from ur heart.
Ta fashe da dariya.."not really,nayi hakan ne cos u where faster dan ur shoulder,but amman hajiya zubaida really deserve this..
Hamdallah ya shiga yi domin kuwa yafi kowa sanin ilham duk da bata ta'ba wani abu makamacin hakan ba...
Tsakalarshi tayi da yatsanta ganin ya shiga duniyar tunani.."kai nake sauraro,wata alfarma kake nema?

Ya matso gab da ita ya ra'da mata magana a kunne.
tureshi tayi da dukan karfinta...u can't b serious!,ta fada tana me hararansa.
Ya shiga yi mata dariya tare da komawa ya zauna dai-dai.
Ta kara dubansa "do u really mean what just said'?
Sai da yayi dariya me isan sa, sa'anan yace "no, i'm just kiding,na rama abinda kika yi min ne yanzun......besides kinfi kowa sani na,ni ba mutumin banza bane.
Ajiyar zuciya tayi "ok.....now lets be serious,ka fada min abinda zaniyi maka. Nima sai na fadi nawa sabida ina son as soon as possible da mun isa nigeria na dauki mataki.
Ok,...ni fa ba alfarma daya kawai nake so da'ga garekiba...
Ok, ka fade su kawai....
sun kai hudu zuwa biyar fa,zaki iya?
Kai ta da'ga..tareda fadin , lissafo su kawai.
Shiru yayi yana me dubanta.
Ita ma shi take kallo,tare da'ga masa gira😉,kai nake sauraro fa.

Zani fada maki, amman kafin nan, naki alfarman sun kai nawa?
Tayi murmushi tareda da'ga masa yatsarta🖕🏻, daya kacal ta fada.
Ido waje yace "u mean it?
eh....ta fada a takaice.
Cikin jindadi yace first of all, will u marry me?

Kai ta da'ga..."na amince"
tsunbul ya mike kamar wanda kunama ya sa'rah...ya hade hanneyensa yana me fadin 'Alhamdulillah'...
ta jawo shi ta zaunar  tare da fadin sai kuma abu na biyu.

Abu nabiyu....na biyu....hmmmm na biyun shine  kiyin min alkawarin zama da ni har abada.
Ta sake da'ga kai,ba tare da ta tanka ba.
Sai kuma na uku...ta fada.
Na uku.....na ukun .....shine ki fadamin yanda kikayi alokacin da kika batar dani...u 've promised that b4.
Ta da'ga kai wannan karon ma.
Sai me kuma?
Ki fadamin yanda kika yi kika sace takardu gun mahaifinki,kuma wadanda suka taimaka maki hakan ta faru.
...ok ok angama, ur majesty ta fada cikin zolaya.
Ta nuna masa hannunta da take kirge dashi.."sai ta biyar? Ta fada...
Uhmmm uhmm🤔...na manta,idan na tuna zani fada maki.
Ok ok...su kenan abinda kake son nayi maka ko?

Sure.!..su kenan ya fada cikin farin ciki.
Yanzun sai ki fadamin naki alfarman da kike nema..

Alright,kamar yanda na fada maka, nawa alfarman daya ne kacal,kuma simple and short.
Eh..eh..eh..inajin ki
so nake ,idan mun isa nigeria ta ta'ra min iyayenmu da yan uwa duka, ciki harda hajiya zubaida.
Waro ido yayi yana me dubanta😳....ya jima a haka sa'anan yace toh shi kenan zanyi haka inn'shaa'Allah.

          **           **      **
Mamee ce tsaye ,ta rungume hannayenta sai kai da komowa takeyi....duk ta rasa me keyi mata dadi .isowarsu ilham kawai take jira.
Tana nan a haka jirgi ya iso,tayi hamdala tare da samun guri ta zauna tana jiran fitowarsu.

Cikin kasaita suke taku, da ka gansu,ka gan wayayyun masoya.
Ba zato sukayi karo da mamee, da sauri kuma a tsorarce Hisham ya saki hannun ilham da ke cikin nasa.
Ya risina ya gaida mamee, ta amsa a yayinda take kai duban ta ga ilham wace ke shirin gaida mamee din....ba tare mamee ta jira gaisuwar ilham ba ta mika mata hannu "ina wasikar?
ta sa hannu cikin jakar,ta ciro wasikar tare da mika mata.
A nan mamee ta bude wasikar ta fara karantawa.
 Ilham ta matso kusa da ita da fadin" da kin hakura mu karasa gida.
Kai ta girgiza ba tareda ta dube ta ba.
Ganin bata da niyar motsawa ,ya sanya ta rike mata hannu "toh mu karasa cikin mota mana.
A hanyarsu ta zuwa inda ta yi parking mota ta mikawa Hisham makuli.
suna isa gun motan ta bude gidan baya ta shige, hisham da ilham ne a gaba.
Hanyar gidan mamee dake unguwan rimi suka dosa,sai a sanan ta fadawa Hisham ai gidan Babanta zasu tafi..
Gidan kaka kuma?...ilham ta fada cikin mamaki.
Ba tare da mamee ta amsa ta ba,ta cigaba da karatun wasikar.

A haraban gidan  suka tarar da mahaifin mamee....zaune yake kan kujera.
Yana hangen motan su ya mike cikin annashuwa.
A tare suka shiga cikin falonsa, bayan sun gaisa, cikin matsuwa yake tambayar ilham abinda kakarta ta bar mata..
Gyaran murya tayi,..."takardun gidaje ne,da zoben diamond,sai kuma wasika.
Shima din cikin ka'guwa ya nemi sanin abinda ke rubuce a wasikan.
ILham ta kai kallon ta ga mamee wace tunda suke cikin mota ta fita hayyacinta,duk da tayi kokarin boye wa.
TA maida kallonta ga kakanta "wasika na hannun mamee.
YA dubi mamee ,wace a lokacin take kokarin boye damuwarta,amman tuni ya fahimci halin da take ciki.
ME ke cikin wasikan?....ya fada cikin sanyi murya.
Tayi kiran ilham,ta mika mata wasika tare da umurtanta da karantawa Baban ta.

TANA fara karanta wasikar, hajiya babba ta shigo falon,don haka ta dakata,suka gaisa, ta kuma nemi guri ta zauna, sannan ta sake farowa daga farko.

*Assalamu alaikum..! Ya ke me kyan halitta. Dukan godiya da yabo sun tabbata ga Allah me rayawa, da ya raya ki, kika sami damar karanta wannan wasikan.*
     *a yau da kika cike shekaru 23years a duniya,ina me yi maki fatan alkhairi duniya da lahira.*
     *na so ganin tasowarki, da girmanki. ina da tabbacin kin zama mace me kyan halita...ina son ki sosai,ina sonki A'isha, sai  dai   Allah ba zai bani damar nuna maki wannan soyayyar ba*
       *ina da tabbacin kin girma da yalwan ilmi da basira,ina kuma kyautaton zaton ke me hankali da fahimta ce*shi yasa ban bar wa kowa wannan wasikan ba,face ke.
   *ya' Ke A'ishatul-ilham, na zabi na bar maki wannan wasikan ne domin na karanci baiwan fahimta da Allah yayi maki,ina kuma kyautata zaton ke ce kawai zaki kubutar da mahaifinki ki kuma tsirar dashi da'ga mumuna zargi da ke tsakaninsa da mahaifiyarki,har sauran yan'uwanki da kuma sauran kawunki.*
      *na kasance cikin damuwa da takaici a lokacin da na fahimci soyayyar da mahaifiyarki take yiwa mahaifinki..burina a lokacin shine ta sami ingantacen ilimi..ganin soyayyarsu na shirin rinjayen karatun ta,ya sa na shiga damuwa, sai dai mahaifiyarki tayi nisa ,bata jin kira.*
  *damuwata ta cigaba har ta kai ga haifar min ciwon zuciya, wanda nima ban farga dashi ba,sai alokacin da yan'uwa da abokan arziki  suka sanya ni gaba suna cecekuce akan Allah shi waddai da auren iyayenki,na shiga matukar damuwa,wanda ya haifar min tsananin ciwon zuciya don haka na kai kaina asibiti,nan likita yake shaidami,ya kuma bani shawaran da na rage tunane tunane hakan zai sa na sami sauki.*
*na sami kwanciyar hankali ne bayan auren iyayenki,ganin irin soyayyar da shakuwar da sukeyiwa juna..na kuma fahimci mahaifin ki mutumin kirki ne ,hakan ya sa ya shiga rai na sosai.*
*Muna a haka kwatsam,na fara lura da yanayin mahaifiyarki, da ga alama da abinda ke damun ta nemi sani sai ta boye min,don haka na fita sabgar ta.*
   *mahaifiyarki ta shiga damuwa da'ga lokacin da ta sami labarin mahaifin ki zai kara aure...damuwarta ta sanya na rasa natsuwa, a koda yaushe cikin tunani nake.*
*nema nake da rokon Allah ya kare ta da'ga shairin masu shsirin domin daga lokacin da na sami labarin aurensa na kasa samun kwanciyar hankali,zuciyata kuwa sai rayamin take wannan auren ba ta lafiya bace.*
   *tafiya ta yi tafiya, mun wayi gari mahaifinki ya aikowa mahaifiyarki takardan saki. Gabaki dayan mu, mun shiga tashin hankali duk da munyi kokarin tausan zuciyoyinmu. Dalilin haka ciwon zuciya ta ta dawo sabuwa.*
*har tana barazanar bugawa,gashi mun kasa sanin dalilinsa na yin hakan*
   *tsananin ciwo da rada'di da nake ji a kirji na yasa na yanke shawaran zuwa ganin likitan mu,da ke kasar landon. A ranar da zani tafi bayan na kammala shiri,me gadi yayo sallama. Ya sanar da cewan nayi bako a kofar gida....nan na umurce shi da ya fadawa ko waye da ya shigo cikin gida.jim kadan ya sake dawowa, wai bakon yace ba zai shigo ba.*
   *don hakana yafa mayafi na fita waje...ina ganin wannan mutumin na tsincin kaina cikin matsanacin faduwan gaba,sunayen Allah na shiga ambatowa har na karasa gunsa*
    *bayan mun gaisa nayi masa nuni da gurin shan iska,don haka muka karasa gurin muka zauna*
    *sunana bilyaminu, ni direban gidansu zubaida ne. Na soma aiki a gidan tun sa'anda zubaida na yar' shekaru goma sha biyu don haka duk wani sirin su a tafin hannu na yake*
   *na dakatar da shi da kuma tambayarsa,shin sun aiko shi ne?*
     *a'a.....ya fada tareda yin shiru kamar me tunanin wani abu,sai da ya dauki tsawon lokaci sa'anan ya da'go ya cigaba da fadin a takaice dai kuma kamar yanda na fadamaki, na kasance direban su duk inda zasu tafi a duk fadin kasar nan ni ke kaisu,idan ma ba da mota za'a tafi ba, toh ni ne me rakiyah sabida yarda da shakuwa da ke tsakanina da su...hakan ya bani daman sanin su da kuma duk wani sirinsu*
  *wadannan  mutanen sun dade suna miyagun ayyuka,wanda nake sane ko nace tareda dani sukeyi yinsu. Wata sa'in ma ni ke nuna masu hanya.*
  *a lokacin da zubaida ta hadu da alhaji Buba ta nuna tana son sa, sai dai shi ba bata fuska ba don haka ta dawo gida ta sanarwa mahaifiyarta,nan mahaifuyar ta ta nemi shawarata, nan na basu shawaran hanyar da za'a bi don samun kansa...garin sakwato muka nufa gun wani malami,wannan malamin ya fada mana zaiyi mana aiki, amman bashi da tabbacin aikin zai yi tasiri sabida katangar soyayayr matarsa dake gine a zuciyarsa zatayi wuyan rushewa.*
  *kana nufin kace katangar bata rushuwa?*
    *dariya yayi yace ba haka nake nufi ba,za ta rushu amma fa zata dauki tsawon lokaci..sa'anan wannan bawan Allah nan fa asiri baya ci a jikinsa sabida kakaninsa sun bashi tsari tunda yana dan jinjiri*
     *cikin ta'be baki zubaida tace iya kuma matar fa?...ba sai kayi aiki ta gefenta ba*?
     *nan malamin yasake murmushi tare da fadin,ai gwara ta gefensa da sauki bisa ga nata. Watau ita wannan baiwar Allah wani jinnu ya shiga cikinta wani lokaci a jeji,wannan jinnun ba me cutarwa bane,domin kuwa a lokacin an cutar da ita ne,sai ya tsinci kansa da tausaya mata don haka ya shige jikinta don tsareta da kuma kare ta a duk lokacin da wani abu me cutar wa zai same ta*
   *a fusace na dubi malamin ganin maganarsa bata da ma'ana, kana nufin bukatun mu baza su samu biyawa ba kenan?*
*da haka muka baro garin sokoto rai bace,mun cigaba da binciken malamai da bokaye wadanda aikin su  ke ci,sai dai cikin rashin sa'a duk inda muka nufa abu guda ko nace iri daya suke fadi*
     *haka yasa zubaida tsananin damuwa,wanda mahaifiyarta ta shiga tashin hankali, don haka ta takuramin akan na binciko masu boko,wanda zai gagauta yi masu aiki...cikin sa'a na sami labarin wani boka mazaunin kasar nijar,na sanar wa mahaifiyar zubaida don haka ba'a bata lokaci ba,muka shirya tafiya zuwa gun wannan bokan.*
    *abinda sauran bokayen suke fadi,ya fada shi dinma, sai dai shi yana da tabacin zamu sami biyan bukatu amman fa ba karamin abu za'ayi ba,kafin bukatun su biya.*
     *cikin kankanin lokaci boka ya fara aiki,kuma nasara ta samu,abu biyu zuwa uku ne suka gagara,..na dayan rashin nasaran rushe katangar soyayyar matarsa, na biyun ,a cewan hajiya zubaida ayi masu aiki matar Alhaji buba ta shiga duniya ita da ya'yanta*

Nan mutumin nan ya dago ya dubeni ya cigaba da fadin duk wani abu da kuka gan sirikin ku yayi ba yinsa bane, har wasu da'ga cikin yan uwansa sai da akayi masu asiri tukun...don haka ku gagauta nema masa taimako.
Ni na tuba, na tuba da wannan shirkan,na kuma tausayawa duk wanda ya shafa, shi yasa na neme ki...wallahi azeem mafi muni asiri sukayi masa wanda ban sanar dake ababe da hanyoyin da suka bi ba don cimma burinsu domin kuwa idan na sanar dake ba zaki runtsa ba...
Duk bokayen sun sanar mana soyayyarsu ba zai rushe ba har abada,don haka ina kyautata zaton wataran zai kawo karshe amman kuma kafin nan wadannan mutane suna iya samun nasara akan yar'ki don baza su hakura ba har sai sun cimma burinsu.
Mikewa yayi da ya kai nan,na mike ina me yi masa godiya cikin sanyi murya.
Bayan tafiyan wannan mutumin na shiga ru'dani...ina me matklukar tausayawa diyata haka yasa na rasa kwanciyar hankali na kuma kasa sanar wa kowa bare na nemi shawara.
Addu'o'i na shiga yimata ba dare,ba rana....
ina kuma kai abinci da kudi makaratun ayi sadaka da kuma sauke wa iyayen ki alkur'anin me girma,don shine kawai mafita alokacin sabida ban iya harkan malamai ko bokaye ba.
Sannu a hankali na fara jin radadi a kirji na,idan na ta'ba sai na ji kamar ta kumbure,ganin haka yasa na nufi asibiti, likitan da kansa ya tausaya min da halin da nake ciki, ya kuma shaida min na kamu da ciwon zuciya sosai kuma zuciyata na iya harba wa a kowani lokaci..
Na matukar tausaywa ya'ya na don suna iya rasa ni at any moment.
A lokacin nayi kokari na fahimtar da mahaifiyarki amman ciwon so ya makantar da ita ta kuma kurmance,don haka na yanke shawaran rubuta maki wannan wasikan,idan har xuwa lokacin da kika sami wannan wasikan abubuwa basu daidaitu ba,na bar maki komai ki cigaba daga inda na tsaya don ganin komai yayi daidai.
daga karshe wannan  zoben💍,gift din aurenki kenan
takardun gidajen kuma na sauran jikokina ne..ki kula da mahaifiyarki.
                       *kakarki*
kuka sosai ilham takeyi,bayan da ta kai karshen wasikar.

toh nima dai me rubutun na tausaya masu, ku biyoni don jin matakin da ilham zata dauka.

No comments:

Post a Comment

Designed by Jide Ogunsanya.