Pages

Friday 2 March 2018

Page39 of SOYAYYAR MU👫

SOYAYYARMU 👫.
            By Ganarious.
Page3⃣9⃣

👉🏼 Annabi (s.a.w), yace: duk wanda ya nemar wa muminai maza da mata gafara,Allah zai bashi lada akan ko wane mumini da muminai..."Dabarani ne ya ruwaito shi daga ubadatu(rt)...Allah shi gafartama al'umman annabi (s.a.w).

       **          **         **
  Bincike ya tabbatar da cewan lallai ilham ce magajiyar ajiyar da kakar ta tayi.don haka ranar zagayowar haihuwarta ake jira ta sami cire ajiyar.
Tun isawarsa take lura da hisham,ta karinci damuwar da yake tattare da shi.
Duk yanda ta so ta cije ta share shi ta gagara,har sai da ta kai ga tambayarsa damuwarsa.

"Iyayenmu sun yanke shawaran hada ni aure da Hindi,sabida kin ki amincewa."
Tsuki tayi "damuwarka kenan,dama?"
Kallonta yakeyi tare da da'ga kai.
Hmmm.....gwara kam ka amince,kar kayi 2zero,domin kuwa ni bazan taba aurenka sabida tuni na cire ka araina,nakuma daina sonka.
Karya kike yi...ya fada cikin da'ga murya kuma rai a bace..ni kadai kike so,ni kadai kike so.
Shiru tayi tana kallonsa ganin yanayinsa.
Sun jima ba wanda yace da wani kala...
Kama yatsunta yayi "ya ya kike ganin rayuwata zata kasance da wata idan ba ke ba?.kin fi kowa Sanin cewan bazani taba son wata ba idan ba ke ba,please ilham ki amince muyi aure.

Mahaifin haj. Zubaida yayi kiran Alh. Buba.
A offishinsa alhaji buba ya sameshu suka gaisa.
Bayan gaisuwan mahaifin haj. Zubaida ya shiga baiwa alhaji buba hakuri akan zargin da yake masa...ya kuma daukan masa alkawarin bincike akan al'amarin nan da yasa me su,sabuda ya alama akwai sa hannun wani.
Tun da ya fara maganarsa har ya kai karshe alhaji buba me tamka ba,sai kallonsa da yakai.
Ya dubi alhaji buba yace "kana jin maganar da nake yi kuwa?
Cikin lumshe ido ya da'ga kai tareda fadin "ina jinka alhaji."
.....toh...maganar da nayi maka a gidan kurkutu cewan zani raba aurenka da diyata,bacin rai ne yasanya ni fadin haka, don haka kayi hakuri ku kuma ciga ba da zamanku yanda kukeyi a baya.
Yana cikin magana sekatariyarsa ta budo kofa,tayi masu sannu da zama sa'anan ta sanar masa yayi bakuwa mace..
Cikin mamaki yace wacece?
Ta da'ga kai, alaman itama bata sani ba.
Ok ...ce mata ta shigo.
Ta juya ta fita daga offishin.
Kafin ya cigaba da maganat,har an budo kofa,don haka ya dakata da maganar yana me duban inda ake bude kofa.
Tana budo kofa sukayi ido hudu...duk da A.c kusan uku da juma fankar da ke office din bai hana zufa karyowa daga jikin sa ba.
Ganin yanayin da ya shiga lokaci guda,ya sanya alhaji buba juyawa don ganin wace zakanya ce.
Ta karaso gun kujeru ta ta zauna ba tareda tayi masu sallama ba,ki ta gaishe su ba sai yatsine yatsine da takai.
Mahaifin hajiya zubaida ya dubi alhaji buba yace "tafi zan neme ka anjima".
Daga shi sai ita a cikin offishin,bayan ficewan alhaji buba...rai bace ya dube ta.."me yasa zakiyi min haka..?ina zaman lafiya da iyalina zaki tarwatsamin su?
Uban harara ta banka masa,hade da jan tsuki "sannu me iyali..,kaji ko nace sannu me iyali,toh wallahi ka sa a ranka ba kai ba zaman lafiya da iyalinka muddin ba ka dauki ya'ya na da muhimmanci ba....infact,sonake ka basu hakinsu na uba,kuma zasu dawo gidanka da zama...sa'anan inason ka gaggauta cika alkawarin aurena da kayi.
Shiru yayi yana binta da ido,domin kuwa yana sane da ko ita wace ce.
Nan ta gama banbamin ta tareda mikewa "ka kasance cikin shirin tarban mu,ni da ya'yana"..tana kaiwa nan ta juya zata fita,sai kuma ta dawo tana dubansa.
"Wata biyu kenan baka aiko mana da kudin abinci ba sabida haka kudin wata biyun nan za ka bani a yanzun kuma,sabida shi na zo karba.
ba tareda yace wani abu ba ya jawo durowan gefen sa.
Bandir din dari biyar-biyar yaciro,tare da mika mata sa'anan tayi tafiyarta.

         **          **        **
Ilham da Hisham ne a bus...ya kwantar da kansa a kafadarta ya na me daukansu hoto(selfie)..kana ganin fuskokinsu zaka fahimci cewan suna cike da farin ciki marar misaltuwa sakamakon ranar haihuwarta da ta zagayo.
     A bus-stop dake gaban offishin House of p.o.p, bus din ya tsaya,hisham ya mika mata hannunsa,ta dubeshi tana me yimasa lallausar murmurshi a yayinda ta saka kyawawan yatsunta cikin hannunsa suka sakko daga bus din.
Rike yake da hannunta👫 gam...kamar ance masa za'a kwaceta,har sai da suka shiga cikin offishin sa'anan ya saki hannunta.
Wani daki aka kaisu me dauke da wasu ababe kamar akwatai,sai da wannan akwatan da bangon daki yak hade.
Mutumin da ya rako su dakin ya duba lambarta sa'anan nuna mata inda akwatin ta yake tare da mika mata makulin.
Bayan ta bude kofan akwatin sai ta gan screen hade da bottons kamar computer, mutumin ya taimaka mata ta kuna, sa'anan ya umurce ta da shigar da sunarta sa'anan ta sa babban yatsan ta a saman screen din.tayi thumbprint 👍🏼
Tana yin  haka kuwa abin ya bude kansa..
nan da nan ilham ta tuno shekarun baya,duk da bata da wayau sosai,ta tuna kakarta ta zo da ita nan,kuma yanda tayi a yanzun hakan tayi lokacin baya...

Envelop da wata karamar kwali suke cikin akwatin...jiki na rawa ta ciro su,tana kokuwar budan envelop din.
Mutumun ds ke tare da su ya dakatar da ita da fadin "da zarar mutum ya cire abu a wannan dakin,ba'a yadda ya kara ko da sekan daya ba,don haka ina rokonku da ku fita waje...yana fadin haka ne a yayinda yake masu nunin hanyar fita da hannunsa.
Sun dubi juna tukun, sannan hisham ya kama mata hannu suka yi waje.
Bayan sun fita haraban offishin,sukayi cirko cirko suna tunanin inda ya dace su tafi dun budan wannan envelip da dan kwali da suka ciro.
Hisham a gidan abokinsa sameer ya sauka,ita ma ilham gun kawarta tayi masauki.
Hisham ya kawo shawaran da su tafi gidan abokinsa ta bude envelop din a can,
Kai ta girgiza..."a'a,zai fi mu tafi gidan da na sauka.
no...no...kinsan yusrah da jama'a,na tabbata a yanzun haka dakin ta cike yake da yan'mata,ba zaki samu kadaice wa.
So please ki biyo ni mutafi gidan sameer,i can asure u that hanzun haka ma baya gida.
Tayi marhaba da shawaransa domin kuwa dakin yusrah baya raguwa da mutane,don haka ta yanke shawaran binsa.
Sun tarar sameer din ma baya gida,ya dube ta tare da'ga mata gira...u see🤷🏻‍♂,I told u he wunt be arround..
Cikin rawan jiki ta nemi guri ta zauna,a yayinda take kokarin bude envelop din.
Shima din zama yayi tare da tsira mata ido,a lokacin ta ciro farar takarda da'ga envelop din, da alama wasika ce.
Ajiye shi tayi gefe,ta ciro sauran takardun dasuke ciki ta duba a tsagaice,suma ta ajiye su gefe.ta sake duban envelop din ba ragowan takardu a ciki don haka ta dauki karamar kwali ta fara budansa a tsanake.
Tana budan kwalin,dan karamin box ne kamar ta sa dankune,ko agogo ko zobe don  haka ta bude box din .
💍zoben diamond💎,ne a ciki.
Cikin dafe kirji ta dubi Hisham wanda daman banda kallonta ba abinda yakeyi.
"It's diamond Ring"😳....ta fada cikin mamaki.
Ya mike daga inda yake zaune ya dawo gefenta,karban zoben yayi ya duba .
"Allah ya taimake ki mun zo nan,inda ba mutane."shine abinda kawai ya fada a yayinda ya sawa zoben ido...ya lura da rubutun cikin zoben...
"Oh my Goodness!😱...sunanki ne fa a rubuce.ya fadi haka cikin mamaki, ayayinda yake kokarin nuna mata sunan.
*A'sha*..shine a rubuce cikin dutsen,..
This is serious...ta fada,tayi ajiyar zuciya tareda fadin it might be for my mum.ko ka manta sunarta Aisha itama?
Oh..sorry,hake ne.ya fada shima,ya cigaba da fadin "yanzun dai bude wasikar  ki karanta.
Ta dauki wasikar jiki na rawa ta fara karantawa.
Tana karantawa tana hawaye,a haka har ta kai karshe..ta fashe da kuka me ratsa jiki,shi daman gogan a matse yake da ta gama karantawa  don jin dalilin kukanta.
Kukan ya hana ta yi masa bayani,sai mika masa wasikar tayi,shima ya shiga karantawa.
Ya gama karantawa ya rungumeta yana me shafan gadon bayanta suna a haka mamee ta kira.
Ilham ta share hawaye,tare da kafa wayar a kunne.
Cikin dasasshen murya tace "hello mamee"
"Hello ilham kinyi kuka ne.....meya faru? Mamee ta nemi sani.
Shiru ilham tayi sabida bata san daga ina zata faro wa mamee bayani ba.
"Babynamesake"...Mamee ta sake fadi,jin tayi shiru
"Na'am mamee"
"Me ke faruwa?...kin je house of p.o.p din?
Eh....daga can nake yanzun.
Tau bani labari....me mamata ta ajiye a gurin?
Hmmmmm...mamee kiyi hakuri,idan na dawo zaki gani.
"Har sai kin dawo...kinsan yanda na matsu kuwa,har babana ma ke kawai yake sauraro.
Toh mamee...da ku hakura,gobe inn'shaa'Allahu, zamu biyo jirgin yan kasuwa.
Toh shi kenan Allah shi kaimu.
Ameen ta fada...
Har zasuyi sallama,sai kuma mameee tace wa ilham" ina hisham?
Gashi nan, ta maida mata.
Ok,ina gaida shi....da fatan ba guri daya kuka sauka ba ko?
Eh,kowa da inda ya sauka.
Toh hakan yayi kyau....sai kun iso.
Nan sukayiwa juna sallam suka ajiye wayar.

             ***            ***
Tun sa'anda alhaji buba ya fito daga gidan kurkutu bai sa kafarsa a gidan da surukinsa ya bashi ba.
Gidan goggoji ya koma da zama.
Hajiya zubaida tayi lallashi akan ya komo ko sabida ita,amman yayi kememe...sai alkawari ya daukan mata cewan zai gina gidansa sai su koma ciki.
Hakan na kona mata rai,ba kuma abinda zatayi sai ta shiga ganin laifin mahaifinta.

Yau ma a gidan goggoji ta same shi,yana ganinta ya shiga yi mata murmushi,ita ma ta maida mass tareda ajiye kwandon abincin da ta kawo masa a gabansa.
A ko da yaushe idan ta zo sai ta lallashe kan cewan ya zo su tafi gida,shi kuma ya dau alwashin cewan ba zaya koma gidan ba.
Suna cikin hira ta bude hakarta,chek(cheque) ta ciro wanda ke dauke da rubutu iya adadin kudin da za'a cira daga banki...miliyan dari da talatin ne a rubuce.
TA mika masa ya sa hannu ya karba yana me duban chek din.
Bayan ya gama duba wa,ya maida kallonsa gareta "wannnan kuma,na menene?
Tayi murmushi sannan tace kudi ne da zaka sayi fili ka kuma fara gini...wallahi na gaji da ganinmu a haka.
Yayi dariya....ya kama hannunta ya maida mata da chek din ciki.
"Kiyu hakuri,nima na gaji da ganin mu a haka,amman inn'shaa'Allahu nan ba da dadewa ba komai zai koma dai dai.
Ta dubi chek din ta dube shi...."me kake nufi da maida min da chek din?..ta fada fuska a murtuke.
"A gaskiya bazani boye maki ba,duk wani abu da zai zo daga mahaifinki,ba zanyi marhaba da shi ba,kuma.....
Ba tareda ta bari ya karasa maganarsa ba,ta taryeshi da fadin "waya fada maka mahaifina ne ya bada kudin?
Shiru yayi bai amsa ta ba.
Nan ta marairace masa tana fadin wallahi tallahi kudina ne,don Allah ka karba kayi mana gini mu koma ciki.
ganin bashi da niyar karba yasa ta mike rai bace ta shiga cikin dakin goggoji, tarar da ita tayi kwance, sai dai ba bacci takeyi ba....ta fashe da kuka.
Nan goggoji ta mike zaune tana tanbayar ta mike faruwa.
Ta fada mata abinda ya faru tsakaninta da alhaji buba.
hakuri da nasiha goggoji ta shiga yi mata.
"Ni gaskiya kiyi masa magana ya karbi kudin,sabida ba shi wata hanyar samun kudi da ta wuce ta karkashin mahaifina,idan ba haka ba ko har sai yaushe zai sami kudin yi mana gini...
nan ma hakuri goggoji take bata.."kiyi hakuri, buban ne da taurin kai,ko da kuwa zanyi masa magana,ba za shi saurara ba sabida ya riga da ya sawa ransa hakan...
   Rai bace ta bar gidan goggoji,gurin mahaifiyarta ta nufa,da isar ta kuwa ,ta sa mata kuka.
Nan ta shiga lallashi itama.
"Gaskiya na gaji da rayuwan nan,na kasa gane me ke faruwa da mu,kuncin yau daban,ta gobe wata kala ce..duk na rasa farinciki na...tana  maganar ne a yayinda take shasshakan kuka.
"Me ya faru kuma yanzun?
"Buba ne...bubane,wai shi duk abinda ya fito daga gun babana baya so"
ciki har da ke kenan,mahaifiyar ta fada.
shiru tayi bata amsa ba.
"Ki kwantar da hankalinki,kiyimin bayanin abinda ya faru.
"Ni dai so nake ki shirya mu tafi gun bokan nan naki na nijar, da alama asirin da yayiwa Buban ya daina aiki,don haka sai ya sake yi mani wani.
...naji,amman har yanzun baki fada min abinda ya faru a tsakaninku ba.
"Kudi na kai masa,tunda ya ki amincewa da ya koma gidan da mahaifina ya bashi,na bashi kudin da yayi gini shine ya ki karba.
mahaifiyar ta tabe baki tare da fadin "matsiyacin banza,shin wai dole ne sai kin rayu da shi.....ki sallameshi ya tafi, ki raba kanki da tsiya,wata kila ma idan kinyi haka kika sami wani zaki sani haihuwa,domin rashin haihuwan nan naki ina zargin matsalan daga gurinsa ne.

Rai bace  tace "Ba shawaranki nake nema ba!..kin kuma fi kowa sanin yanda na dauki Buba,don haka ko da wasa kar ki kara fadin na rabu dashi,haihuwa kuma ba damuwa ta bace,mudin ina tareeda Buban.
ganin yanda ranta ya baci ya sanya mahaifiyar ta shiga bata hakuri cikin sanyi jiki,ta kuma yi mata alkawarin shirya masu tafiyar.

                 ****
Baba Yusuf da Baba lamido ne zaune a falon goggoji,har da Alhaji Buban...
banbami sukeyi...."wannan ya maida mu shashashu,yau kwana hudu kenan muna neman lambar wayarsa baya xuwa....fadin baba yusuf
cikin yanayin damuwa goggoji tace "kun duba gun abokansa?
duk mun aika a duba mana shi baya nan.
Toh allah yasa lafiya, ta sake fadi kamar me shirin yin kuka.
tsuki Baba yusuf yayi tare da fadin yana nan lafiya,iskancin sa ne kawai ke damunsa,don haka kar ki sawa kanki damuwa.
tayi ajiyar zuciya sa'anan ta dubesu "ni da kun kyale yaron nan,tunda baya son wanan hadin da kukayi...ku barshi ya aure wace yake so mana..
jiya jiyan nan na bayar da kudi aka hado kayan lefe,don haka aure kam ba fashi...fadin baba lamido
"Ni dai da so samu ne ,ku hakura da wannan aure.
Shiru sukayi basu amsa ta ba.

Hisham ya gama shirin sa tsaf,ya shiga kiran layin ilham bata da'ga ba..don haka yayiwa sameer sallama,sa'anan ya kama hanyar gidan yusrah.
yana isa ya kwankwasa masu kofa,yusrah ce ta zo ta bude masa...tayi masa sannu da zuwa ,sa'anan ta bashi izini da ya shigo ciki.
a falo ya zauna,ita kuma ta shiga ciki don kiran masa ilham...
Bai jima da zama ba ilham ta fito,da alama tashiwarta kenan daga bacci.
dubanta yakeyi,a yayinda take soshe soshen idonta,ta karasa gefensa ta zauna.
"Kin manta da batun tafiyar mu ne?...ya tambaya.
ta da'fa kai🤦🏻‍♀,sannan ta kai dubanta gareshi,irin kallon da takan yi masa yaji hankalinsa ya tashi,tayi masa...
"Ban manta ba wallahi,na kwana da zazzabi ne,ban kuma sami bacci ba sai da safen nan.
a hanzarce ya matsa kusa da ita,ya sa hannunsa a goshin ta,ta dubeshi,shima din ita yake kallo.
kamar me ra'da yace "me ya kawo haka?.
ta kauda  kanta gefe.
"Sabida wasikan nan ki!..kin sawa kanki damuwa ko?
bata amsa ba ta mike "zan shiga daga ciki don shiryawa na zo mu tafi".
kallonta yakeyi har ta shige,ajiyar zuciya yayi a ransa yana fadin "Allah kadai yasan abinda take shiryawa yanzun kuma,na gode Allah wannan karon iyayena da yan uwana sun tsira,ko da zata dau fansa ne"
Read More »

HOW TO GET A FLAWLESS SKIN USING TURMERIC(KURKUM)

👌🏼HOW TO GET A FLAWLESS SKIN, 👱🏼‍♀🧕🏻 USING TURMERIC (KURKUM)👌🏼.

Soft,smooth, and glowing skin Is the dream of every girl👱🏼‍♀🧕🏻...
Oh yes! Virtually all of us have the habit of complaining that this,and that are disturbing their skin.,well that's why we are human.no one is perfect.
And that's also why I'd decide to share with u halfway of making ur skin flawless, with the use of turmeric known in hausa as kurkum.

Turmeric doesn't bleach, but only soft and gradually  fades out the acne parts of ur skin making (skin) to looks glowing.
U can choose any of this methods, in accordance of what u have indoor.
                  *A*
Things  u need.
*turmeric    2table spoon,
*honey        1table spoon,
*lime juice   2tablespoon,
*milk            2tablespoon,
*yeast          1/2tablespn,
*body lotion,
*body mist o any perfume of ur desire.
*plain flour.

            *DIRECTION*
!~Get ur bowl and spoon,pour ur turmeric, yeast and milk and then mix.

!!~pour ur lemon juice and honey and then mix.

!!!~add ur perfume or humrah,and then ur lotion.
👉🏼 *NOTE*,U can add ur plain flour if the paste is too runny.

   HOW TO USE WHEN UR PASTE IS READY!👍🏼
👉🏼wash ur face (or all of d body ),using warm water..u can also steam ur face.👱🏼‍♀

👉🏼fetch small amount of it and scrub to d face until it's all covered.
Allow for 30-40minutes and then u rub it off and wash ur face.

                *B*
Things u need.
*turmeric.  2teaspoons
*milk.        1
*egg yolk
              *Direction*
Mix ur turmeric together with the egg yolk and milk,making a paste.
Apply the paste over ur face👱🏼‍♀,allow to dry and then wash off.

              *C*
Things u need.
*turmeric 2teblespoon,
*sandal wood 1tablespoon
*honey
*cucumber juice
        *DIRECTION*
Mix all together making ur scrub,paste it over ur face and allow it to dry then u wash of.
👉🏼Note,WHEN using turmeric scrub,u would have to avoid exposing ur skin to the sun.
Turmeric can stain ur palm and clothes.
     Discover GANARIOUS SECRET, By visiting 👉🏼 ganarious.blogspot.com/ and learn more on skin Care tip.💃🏻🧚🏻‍♀
Read More »
Designed by Jide Ogunsanya.