1⃣
Zaune take gaban mamee tana kuka sai sharan majina takeyi, idanuwan gasu daman da girma sai suka kara girma da kunburi don tsabar kuka. Cikin kuka take cewa 'mamee kiyi hankuri don Allah, nayi alkawari bazan sake saba maki ba...mamee dai ko kallon gun da take batayi ba, news pepa ke hannunta tana karantawa, duk da har cikin ranta take jin kukan ilham amman bai hana ta saurare ta ba. Suna cikin haka Anty kulu ta shigo"subhanallah" haba maman A'isha! Wai ke ba ayimaki laifi ki yafe ne? Daga bakin kofa take wannan maganar tare da karasowa ta zauna kusa da mamee.
Cikin nutsuwa tace haba maman A'isha! Me yayi zafi haka? Ki tuna Allah ma anayi masa laifi kuma idan an rokeshi gafara yana yafewa balle dan adam! Yarinyar nan ta jima tana rokonki da kiyimata afuwa amma kinki. Toh ya kikeson tayi? Sai sa'anan mamee ta ajiye news pepan hannunta da daman tunda Anty kulu tashigo bata kalli inda take ba sai a lokacin da tayi wannan furucin.
A sanyaye mamee ta kai dubanta ga anty kulu tace wallahi har ga Allah ah da nayi fushi da ilham amman a yanzun na yafemata bani dai son tana zuwa gun dangina taje can gun yan uwan babanta na yafe masu har ga Allah.
Hmmm...maman A'isha kenan. Allah ya huci zuciyar ki amman da alama baki yafemata ba. Cewan Anty Kulu
Mamee tayi murmushi tace Anty kulu sai kace baki sanni ba! Wallahi na yafemata.
Cikin kuku nace nagode Mamee kuma don Allah ki janye maganar nakoma gun dangin abbana,nayi maki alkawari ba abinda zai sake hadani dasu balle har ayi maganar aurenmu da Hisham. kinji mamee? na fada tare da dan jan jiki zuwa inda take zaune na dafa hannayena bisa cinyarta.
Kinji mamee...ki yafemin don Allah.
Hawaye cike cikin idon anty kulu tace 'oh ni kuluwa,wannan lamarin sai kace a fim? cikin murmushi Mamee ta juyo ta kama hannayena da suke bisa cinyarta ta hada da nata tana murzawa a hankali tace ilham kisan inason ki ko ? Da sauri na daga kai. Tace bazan iya tauye maki hakin ki akan abinda kike so ba sabida nima iyayena basu tauyemin nawa ba duk abinda nake so shi sukeyi kuma shi sukeyi hakan ne yasa nashiga halin kunci ina kuma gudanmaki shiga wannan halin kuma baki fahimci haka ba...
da sauri na katseta da fadin na fahimta nakuma tuba duk abinda kike so shi nake so kuma shi zanyi,wallahi bani ba hisham bana son bacin ranki
Ah ah ilham,banison na zama sanadin gushewar farincikin ki don haka na amince maki ki auri hisham sai dai banison kowani dangina yayi involving a cikin gudun abinda ya faru a baya.
Mamee na tuba kiyafemin
Na yafemaki ilham...ta sa hannu ta share min hawaye.
Mamee nayi alkawari bazan sake hulda dasu ba kinji.
Kai kawai ta gyada.
Mamee tayi murmushi da ta juya ta gan anty kulu na shesshaka kuka "haba anty kulu kaka nayi jika nayi?"
Aiko nan anty kulu ta fashe da kuka ta mussamman tana sharan majina tace "Ya'Allah wadannan bayinka ka yayemasu damuwarsu!"
Mamee tace inn shaa Allah abinda kike tunani zai faru da ilham ba kuyi mata addua.
"Tashi ki shiga ciki kice wa blessing ta kawo wa Anty kulu abin motsa baki" Mamee ta ce da ni
A sanyaye na mike na sami blessing a kitchen tana hada fruits salad.
nace ta kaiwa su mamee idan ta gama.har nakai bakin kofa blessing ta kirani "Anty a'isha kindawo kenan? Mamee ta yafe maki? Zaki auri hisham din?" Yanda ta jero tambayoyin lokaci guda kuma yanayin fuskarta ta kuka-kuka suka bani darifada
"Yes ! Ofcos i'm back blessing. Kuma Mamee tayafemin hamdan! amma kuma bazan auri hisham ba" na ce da ita.
Oh my God...what a pity..
Nan na barta tsaye na wuce zuwa daki: shiga ta daki yayi dai dai da shigowar kira a wayata. da sauri na karasa gun wayan,da karfin gaske gaba na ke ta faduwa ganin me kiran... wayan yayi ruri har ya tsinke karo na farko. Yana tsinkewa nayi ajiyan zuciya tare da fadin hamdan! Zani ajiye wayan kira ya sake shigowa sai dai wannan karon wata zuciyan ta umurceni da na dauka.
Cikin kwantar da murya nayi sallama daga can aka amsa.bayan mun gaisa baba lamido ke tambayata ina nake yanzun?
Ina gidan mamee.
Ok...ita mameen tana gida ne ?
Eh tana nan
Ok fadamata ina nan zuwa yanzun.
"ah ah baba kar kazo" nayi saurin fada
Daga can yace "kar ki damu, magana me muhimmaci zamuyi cikin fahimtarwa,nima banison musake tashin hankali da ita...ki fadamata gani nan zuwa"
Na dade tsaye ina tunanin yanda zanje na fadawa mamee sakon baba lamido. wata zuciyar ta rayamin da na tafi wata kuma nacewa kar ki je.
Samun guri nayi gefen gado na zauna ina tunanin yanda Mamee da baba lamido zasu kwashe sai dai inda na godewa Allah mamme ba me son hayaniya bace shi kuwa baba lamido masifa har da na saidawa. Nayi zurfi a tunanibda neman mafita akan al'amari na sai ga blessing ta shigo. Anty Aisha mutuminan na ranar nan da yatashi dambe da daddy(daddy kanin mamee ne) ya zo.
Na tabbata da inada hawanjini yanke jiki kawai zanyi a gun sabida tsaban razana da faduwan gaba... Addu'a kawai nake yi har sai da na samu natsuwa...blessing na tsaye kaina har zuwa wannan lokacin sai kallona takeyi da fuskar nan me kama da kuka-kuka.
Anty kulu ce tashigo ta samu guri kusa dani ta zauna tare da riko kafadata ta kwantar dani a jikinta
Kiyi hankuri A'isha komai yayi tsanani yana tare da sauki..
Toh anty bansan dalilin dayasa suke tashi hankali akaina ba. bana son bacin ran mamee.
Karki damu Allah zai kawo mafita cikin sauki.tana kaiwa nan mamee ta shigo.
"taso" kawai tace min ta juya.
da taimakon anty kulu na iya mikewa tsaye,anty kulu don Allah rakani
Ba musu tarikemin hannu muka nufi falo.a zaune na tarar da baba lamido,mamee kuma na dane dane wayarta a sanyaye na gaishe shi ya msa min tare da fadin har yanzun kina kukan ko? Toh Allah ya sawwaka!
Bayan sun kara gaisawa da anty kulu ya dubi mamee da har zuwa wannan lokacin dane dane takeyi bata ma ko kalli inda muke ba.
"Hajia Aisha" baba lamido yayi kiranta
cikin isa da kasaita ta dago ido tana dubansa. "yau nazo ne muyi maganar fahimta ba da fada ba. Niyyata na sami yan uwanki sai dai kuma nayi tunanin abinda kikeso shi suke so shiyasa na yanke binta gurinki.
don darajan annabi s.a.w ki bani hankalinki ki mu fahimci juna. ki tuna fa Allah anayimashi laifi, kai!...laifufuka ma kuma yana yafewa. nasan gabaki dayanmu masu laifi ne a gunki muna kuma neman gafararki. kiyi hankuri da abinda ya faru a baya. kar laifinmu ya shafi yaran da basu san hawa ba basu san sauka ba.
Auren ilham da hisham wata hanyace da zai sa mu gyara kuskurenmu...
Gyaran murya Mamee tayi batare da ta bari baba lamido ya karasa abinda yakeson fadi ba.
Naji duk abinda ka fada na kuma fahimci abinda zaka fada. yanda baka son tashin hankili nima haka banaso. Maganar auren ilham da hisham kuma ban hana ba sai dai ina fatan zakuyi abinku can batare da an saka yan uwana a ciki ba. Sa'anan maganar cewa zaku gyara kura kurenku na baya bana so. Kuskure kam anyi, kuma ya wuce don haka kowa ya tsaya inda Allah ya ajiye shi.
shiru baba lamido yayi na dan lokaci sa'anan yace kin tabbata har a zuciyar kin amince ilham ta auri hisham ?
Kai kawai ta gyada ba tare da tace wani abu ba.
Toh alhamdulillah ilham kinji abinda mameen ki tace ko ?
Eh ! Naji baba,sai dai ni yanzun bani son hisham bazan aure shi ba.
Cikin mamaki baba lamido ya kalle ni har zaiyi magana saikuma ya fasa ya girgiza kai tare da fadin shikenan,Allah yasa haka shine alkhairi. sa'annan ya tashi yayi mana sallama ya fice abinsa
Dama ficewarshi anty kulu ke jira ta fara yimin fada.
"Keh! kina da hankali kuwa muna kokarin abu yayi sauki kina kara batawa?
..kubiyo ni a ganarious.blogspot.com/